An Sako Yan Daurin Aure Na Jihar Zamfara Su 29.
Yan ta’adda ne suka yi garkuwa da yan daurin auren 29 makonni biyu da suka gabata a garin Dogon Awo dake kan iyaka da Jihar Sokoto a yankin arewa maso yammacin Najeriya.
Sakataren kungiyar masu sayar da na babban birnin jihar Zamfara, Ashiru Zurmi ya tabbatar da sakin mutanen ga majiyar Popular News Hausa ta AIT.live ta wayar tarho.
Zurmi ya ce an sako mutanen 29 a wannan Alhamis din da yamma, kuma sun hau hanyarsu ta zuwa Gusau.
Saidai majiyar bata bayyana cewa ko an biya kudin fansa ba.
