September 18, 2026

Gobara Ta Halaka Mutane 24 Tare Da Lalata Dukiya Ta Miliyan 600 A Katsina

0

Daga El-Zaharadeen Umar, Katsina

Hukumar kashe gobara ta jihar Katsina ta bayyana cewa an samu asarar rayuka 24 tare da lalacewar dukiya da ta kai ta akalla naira miliyan dari shida sakamakon annobar gobara da ta afku a cikin shekarar 2021.

Baban jami’in hukumar Lawal Haruna Saulawa ya bayyana haka ga manema labarai a Katsina inda  ya ce bangaran kashe gobarar ya yi namijin kokarin wajan tsiratar da rayuka 45 duk a cikin shekarar da ta gabata

Haka kuma ya kara da cewa sun samu rahotannin gobara a fadin jihar Katsina da suka kai 568 a kananan hukumomin 34 na jihar, a ya yin da suka yi kokarin tsiratar da dukiyar da ta kai ta naira biliyan biyu.

“Acikin shekarar 2021 mun samu rahotan gobara kimanin 568 sannan mutane 24 sun rasa rayukansu, an yi asarar dukiya ta miliyan dari shida tare da kubutar da dukiya da ta kai kimanin biliyan biyu” inji shi

A cewarsa wannan bangare na kashe gobara bai tsaya nan ba wajan daukar matakai na dakile faruwar gobara ba, inda ya kara da cewa gwamnatin jihar Katsina ta yi duk abinda ya kamata domin ganin aikinsu ya tafi yadda ake so.

Sannan ya kara da cewa nan ba da jimawa ba, za su fara wayar da kan jama’a ta hanyar gidajen Radiyo da talabijin hanyoyin da za a rika kaucewa faruwar irie-iren wadannan iftila’I anan gaba, musamman karatowar yanayin sanyi da ke tafe.

About The Author

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *