Bayan Rasuwar Hon. Rabe Nasir: Wa Gwamna Masari Ya Nada Kwamishinan Riko A Ma’aikatar Kimiya Da Fasaha ?
Daga El-Zaharadeen Umar, Katsina
Gwamnan jihar Katsina Aminu Bello Masari ya nada kwamishinan ma’aikatar raya karkara Eng Mustapha Mahmud Kanti Bello a matsayin wanda zai kula da harkokin ma’aikatar kimiya da fasaha da kere-kere ta jiha.
Aminu Masari ya amince da nadin kwamishinan don kula da ma’aikatar, har zuwa lokacin da za a nada sabon kwamishina wanda zai dauki cikakken alhakin tafiyar da ayyukan ma’aikatar.
A wata sanarwa da sakataren gwamnatin jihar Katsina Dr. Mustapha Muhammad Inuwa ya sanya wa hannu, ta ce” matakin ya biyo bayan rasuwar tsohon kwamishinan ma’aikatar, Marigayi dakta Rabe Nasir.
Idan dai za a iya tunawa Dokta Rabe Nasir ya rasu ne ta hanyar kisan gilla da wasu da ake zargi da aikatawa akai, lamarin da jami’an tsaro ke ci gaba da bincike.
