September 17, 2026

Kotun Daukaka Kara Ta Dawo Da Dauda Lawal A Matsayin Dan Takarar Gwamnan Jihar Zamfara Na PDP.

0

Wata kotun daukaka kara dake Sokoto ta sanar da Dauda Lawal a matsayin dan takarar gwamna na jam’iyyar PDP a jihar Zamfara.

Tun da farko wata babbar kotu da ke zamanta a garin Gusau na jihar Zamfara karkashin jagorancin mai shari’a Aminu Bappa-Aliyu ta soke zaben fidda gwanin da ya tsayar da Dauda Lawal a matsayin dan takarar gwamna a jam’iyyar PDP, a maimakon haka ta ce jam’iyyar PDP ba ta da dan takarar gwamna a jihar.

A hukuncin da ta yanke, kotun daukaka karar ta yi watsi da hukuncin da babbar kotun tarayya ta yanke a wannan Juma’ar.

Dukkan mambobin kwamitin mai mutane uku na kotun daukaka karar a zaman da suka yi a wannan Juma’ar 06/01/2023 Juma’a sun amince da hukuncin da alkalin kotun mai shari’a Muhammad Shu’aibu ya yanke, wanda ya umarci hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC ta amince da Lawal a matsayin zababben dan takarar gwamnan jam’iyyar PDP na jihar Zamfara gabanin zaben 2023.

Kwamitin ya ce, bai kamata ba ga babbar kotun da ta ƙi amincewa da rohoton hukumar zaben akan zantukan fidda gwani yana mai cewa ba a tabbatar ba duk da cewa mutane suka tattara takardun kuma aka buga kan shafin hukumar zaben.

Da yake mayar da martani kan hukuncin, Dauda Lawal ya bayyana hukuncin kotun daukaka karar da aka yi a Sokoto a matsayin nasara ga dimokuradiyya dama mutanen jihar Zamfara.

Dan takarar gwamnan na PDP wanda ya yi magana ta hannun ofishin yada labarai na Dauda Lawal, ya ce hukuncin kotun daukaka karar nasara ce ba ga jam’iyyar PDP kadai ba, har ma ga daukacin al’ummar Zamfara don kishin samun shugabanci na gari, inji majiyar jaridar Popular News Hausa ta Vanguard.

About The Author

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *