Matan Arewa Maso Yamma Sun Amsa Kiran Uwargidan Ɗan Takarar Shugaban Ƙasa Sanata Oluremi Bola Tinubu A Katsina
Daga El-Zaharadeen Umar, Katsina
Dubun dubatar mata be suka yi dirar farin ɗango a jihar Katsina domin nuna goyon baya ga jami’yyar APC da kuma ɗan takarar shugaban ƙasa Bola Ahmad Tinubu a zaɓe mai zuwa.
Hakan na zuwa ne a daidai lokacin da uwargidan ɗan takarar ta yi taron mata da suka fito daga jihohi bakwai da na arewa maso yamma da suka haɗa da Kebbi da Sakkwato da Zamfara da Katsina da Jigawa da Kano da kuma Kaduna.
Taron ya damu halartar duk wasu masu ruwa da tsaki da da shuwagabannin mata da na wannan yanki domin neman goyon baya jama’a musamman mata da ake yi wa lakabi da masu alƙawari.
Tunda farko a jawabinsa gwamnan jihar Katsina Alhaji Aminu Bello Masari lokacin da tawagar mai ɗakin Bola Ahmad Tinubu ta kai masa ziyara a ofishin sa da ke gidan gwamnatin Katsina ya yaba da irin gudunmawar da mata ke badawa a siyasa.
Gwamna Aminu Masari ya jadadda bukatar da ake da ita wajan jami’yyar APC ta yi nasara tun da daga sama har ƙasa a zaɓe mai zuwa idan Allah ya kaimu da rai da lafiya.
A cewar gwamna Masari sun san wanene Bola Ahmad Tinubu shi yasa suke yin tafiyar kamar rai da ajali saboda a cewar sa, suna sane da irin rawar da ta taka wajen ɗaukaka darajar jihar Katsina da kuma Najeriya baƙi ɗaya.
“Wannan da ma wasu dalilai yasa muke kyautata masa zaton cewa shi zai lashe zaɓe mai zuwa, sannan jihar Katsina zata yi duk mai yiwa wajan ganin Sanata Bola Tinubu ya kai ga nasara” in ji Masari
Da take maida jawabi uwargidan ɗan takarar shugaban ƙasa a ƙarƙashin jam’iyar APC Sanata Oluremi Bola ya yaba da irin karamcin da ta ga Katsinawa sun nuna mata musamman shi gwamna Aminu Bello Masari da sauran jama’a.
Ta ƙara da cewa maigidanta Bola Ahmad Tinubu mutum da yake da kyakkyawan manufofi a siyasa saboda haka ne take neman goyon baya jama’ar jihar Katsina da kuma arewa maso yamma baƙi ɗaya.
“Idan Allah yana maigidana wannan shugabanci zai ƙoƙari wajan inganta rayuwar ‘yan Najeriya wajan samar da ayyukan yi ga matasa da inganta harkar tsaro da ilmi da Noma da bunƙasa tattalin arziki da sauran su.
Bayan ziyarar ban girma da tawagar uwargidan ɗan takarar ta kaiwa gwamna Aminu Bello Masari sun wuce dandalin al’umma domin ganawa da dubun dubatar matan arewa maso yamma da suka taro domin nuna goyon bayan su a wannan tafiya.
An dai gabata da jawabai daban daban daga shuwagabannin da masu ruwa da tsaki a tafiyar jami’yyar APC domin neman goyon bayan jama’a su zaɓi jam’iyyar APC a zaɓen 2023 mai zuwa.
Wannan taro dai ya haɗa manyan ‘yan siyasa musamman mata da suka fito daga jihohi bakwai na arewa maso yamma da kuma wasu daga cikin matan gwamnoni da matan masu takarar kujerar gwamnoni na wannan yanki.
