September 18, 2026

Ƙungiyoyin Matasa Da Mata Sun Yi Gangamin Nuna Goyon Baya Ga Gwamna Buni A Yobe

0

Daga Muhammad Maitela, Damaturu

Gamayyar ƙungiyoyin matasa da mata ne (YOCOPA) a ƙarƙashin jam’iyyar APC, daga ƙananan hukumomi 17 da ke faɗin jihar wanda suka gudanar da gangami tare da jerin-gwano, domin nuna cikakken goyon bayan su ga gwamnan jihar Yobe Hon. Mai Mala Buni, a babban birnin jihar, Damaturu a ranar Talata.

Bugu da ƙari, gagarumin taron ya ƙunshi shugabanin matasan tare da na mata a kowane mataki, kana kuma ya samu halartar ƙusoshin gwamnatin jihar da na jam’iyyar APC a kowane mataki a jihar- waɗanda suka haɗa da gwamnan jihar, Kakakin Majalisar Dokokin jihar, shugabanin jam’iyyar APC da Sakataren gwamnati da sauran su.

A jawabin gwamnan jihar Yobe, Hon. Mai Mala Buni, wanda mataimakin sa ya wakilta a taron; Alhaji Idi Barde Gubana, a taron wanda ya gudana a babban filin wasa na 27 August da ke Damaturu; ya yaba wa matasan bisa jajircewa, hadin kai tare da fatan ganin matasan sun yi gagarumin shirin tunkarar zaɓen 2023 mai zuwa.

A hannu guda kuma, gwamnan ya gargadi matasan da su ci gaba da haɗa kai kuma su guji duk wani abin da zai jawo tashin hankali a jihar a lokacin yaƙin neman zaɓe.

Hon. Barde ya ce gwamna Buni mutum ne mai kishin al’amuran matasa, kuma ya cika dukkan alkawuran da ya ɗauka a lokacin yaƙin neman zaɓe ta hanyar baiwa matasa muhimmanci tare da naɗa su muƙamai a faɗin jihar.

Gwamna Buni ya yaba wa ƙungiyoyin matasa da mata, waɗanda suka shirya wannan gagarumin gangamin tare da nuna cikakken goyon bayan da suke baiwa gwamnatinsa.

A jawabin mataimakin shugaban jam’iyyar APC na shiyya ta ɗaya (Zone A), Alhaji Mustapha Gaidam tare da mai baiwa gwamna shawara na musamman kan harkokin siyasa da majalisar dokoki, Hon. Aji Yerima Bularafa sun jaddada bukatar ci gaba da wayar da kan jama’a kan sabon tsarin zaɓe da INEC ta bullo da shi.

Har wala yau sun buqyaci gamayyar ƙungiyoyin matasa da mata da ke ƙarƙashin jam’iyyar APC a jihar su guji saka kansu cikin ayyukan da za su kawo wa jam’iyyar cikas tare da ƙara zage dantse wajen jawo hankalin al’ummar jihar su zaɓi APC a kowane mataki.

A nashi jawabin, shugaban gamayyar kungiyoyin, Hon. Babagana Alh. Modu (Bature Goniri), ya bayyana cewa manufar taron ita ce nuna amincewar matasa da mata tare da jaddada goyon bayansu ga takarar gwamna Mai Mala Buni da mataimakinsa Hon. Idi Barde da sauran dukan yan takarar jam’iyyar APC, kuma taro ne na dukkanin kyungiyoyin jam’iyyar APC a jihar.

Shima da yake tofa albarkacin bakinsa, Ko’odinatan Hukumar Sake Raya Arewa Maso Gabas (NEDC) a jihar Yobe, Dr. Ali Ibrahim Abbas ya ce matasa a jihar za su ci gaba da nuna godiya da alfahari da gwamnatin gwamna Mai Mala Buni kan yadda yake nuna cikakkiyar kulawa wajen haɗa kai tare da ƙoƙari wajen inganta rayuwar matasa don ci gaban al’ummar jihar Yobe baki ɗaya.

Yayin da a ƙarshe mataimakin gwamnan ya karɓi ɗaruruwan ‘ya’yan jam’iyyar PDP waɗanda suka sauya sheƙa zuwa APC daga ƙananan hukumomin Goniri, Gujba da Nayi-nawa a Damaturu.

About The Author

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *