Daliban Jami’ar Rivers Na Zanga-zangar Mutuwar Abokinsu.
An samu tashin hankali a Jami’ar Fatakwal da kuma Asibitin Koyarwa ta Jami’ar Fatakwal da ke Jihar Rivers, biyo bayan mutuwar wani dalibi da ya kammala karatun digiri kuma sananne a shafukan sada zumunta, wanda aka fi sani da Yemitheplug.
Wasu fusatattun daliban jami’ar sun tare kofar shiga asibitin domin nuna rashin amincewarsu da halin da ya kai ga rasuwar Yemitheplug, wanda har ya zuwa lokacin rasuwarsa dalibin ne dake kammala karatu a jami’ar, inji majiyar jaridar Popular News Hausa ta Punch.
Yemitheplug, mai suna Folorunsho Michael, an ce ya yi fama da ciwon asma, inda aka garzaya da shi zuwa asibitin koyarwa ta jami’ar UPTH, daga nan ya ce ga garinku.
Bayan rasuwarsa, abokansa, wadanda suka fusata, sun shiga zanga-zangar, inda suka datse kofar shiga asibitin koyarwa na wani dan lokaci, tare da bukatar a yi bayanin yadda abokin nasu, wanda suka ce an kai shi da rai ya mutu.
Daya daga cikin abokan mamacin da bai so a ambaci sunansa, ya yi zargin cewa ba duba lafiyar Yemi ba saboda ma’aikatan jinya dake aiki sun ce ba su da iska mai taimaka lumfashi wato (Oxygen).
Wani dalibi, wanda kuma ya nemi a sakaya sunansa, ya shaida wa manema labarai cewa, yana zargin wasa ne da aka yi da majinyacin yasa ya rasa ransa, a daidai lokacin da wani jami’in asibitin ya yi ikirarin cewa Yemi ya riga ya mutu lokacin da abokansa suka kai shi asibiti.
A halin da ake ciki, mahukuntan asibitin koyarwa ta jami’ar UPTH sun jajanta wa ‘yan uwa da abokan arziki na marigayin.
Sanarwar ta ce, “Hukumar UPTH tana jajantawa abokai da iyalan Folorunsho Michael, wanda aka fi sani da Yemitheplug, wanda ya rasu da sanyin safiyar wannan Talatar, 29 ga watan Nuwamba, 2022.
