September 17, 2026

Gobe Kungiyar Mata ‘Yan Fim Zata Gudanar Da Babban Taro A Kano

0

Idan Allah ya kaimu gobe Asabar 23 ga watan Yuli ne a ke sa ran kungiyar Mata masu gudanar da harkar fim ta AKAFA za gudanar da wani babban taro domin shagalin bikin Sallah.

Taron wanda shi ne na farko da Matan suka shirya a kungiyar tasa tun bayan kafuwar ta kusan watanni hudu da suka gabata,.

Kuma ana sa ran, dukkan Mata ‘Yan fim da a ke yin harkar fim ɗin da su tun daga farkon kafuwar Masana’antar zuwa yanzu za su halarci wannan taron.

A wata sanarwa da shugabar kungiyar ta ƙasa Rashida Adamu Abdullahi Mai Sa’a ta fitar ta tabbatar da cewar wannan taron ba a ɗauke wa duk wata Jaruma da take cikin Masana’antar Kannywwod ba, saboda haka suna gayyatar kowa da kowa.

Sannan duk wata jaruma da take da aure ita ma taron nata ne, don haka suna buƙatar ta halarci wajen tare ya’yanta idan ma akwai masu jikoki to su taho da su, domin taro ne na sada Zumunci da kulla ‘yan uwanta.

Taron dai za a yi shi ne a babban ɗakin taro na Meenah Events Center da Misalin Karfe biyu na Rana.

About The Author

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *