An Ayyana Shugabannin tafiyar Bola Tinubu na Jihar Zamfara
Daga Hussaini Ibrahim, Gusau
Masu karin magana na cewa, ba’afafe gora ranar tafiya,yanzu haka Shugaban tafiyar dan takarar Shugaban Kasa na Jamiyyar APC ,Bola Ahmad Tinubu watau (BAT) ta kammala shirinta na fidda sunayan Shugabannin ta na Jihar da na kananan hukumomi, karkashin jagorancin Kodineta na Jihar Hon Tanimu Mada.
Babban Kodineta na Jihar Zamfara,Hon Tanimu Mada ya bayyana, Shugabannin tafiyar kamfen dan takarar Jamiyyar APC na takarar Shugaban Kasa,Bola Ahmad Tinubu tundaga matakin Jiha da na Kananan hukumomi da na gunduma afadin Jihar ta Zamfara.
Hon Tanimu Mada ya bayyana cewa,wannan tafiya tafiyace ta gogagun “Yan siyasa masu sadaukar dakai dan cigaban al’ummar su.wanan ne ya sanya muka zabo jajirtatu wadanda zasu tsaya tsayin daka wajan ganin samun nasara dan takarar mu na Shugaban Kasa a Zane mezuwa.inji Hon Tanimu Mada.
“Hon Mada ya bayyana sunayen Shugabannin tafiyar na Jihar kamar haka, Kodineta na Jihar Zamfara,Hon Tanimu Mada. Sai Manbobinsa goma sha biyar,wanda suka hada da, Alhaj Bashir Atiku Sardaunan Maradun, Hon Kabir Musa Rututu, Alhaji Yahaya Yari,Mafara, Alhaji Samaila Balarabe Anka,Alhaji Isah Umar Tambuwal, Alhaj Lawal PA Yarima, Alhaj Saddam Ruwan Dorawa, Alhaji Yusuf Zugu, Eng Babangida Abdullahi Gusau , Alhaji Musa Yusuf Tsafe, Hon Bello Bakyasuw, Alhaj Surajo Mai Katako Gusau, Alhaji Alasan Aliyu Rijiya, Alhaji Bashir Attaka Gusau da kuma Sakataren tafiyar shine Kwamaret Mansur Sai Shugabar Mata ta jihar Hajiya Kyauta.
Haka kazalikama Kodineta na Jihar Zamfara Hon Tanimu Mada ya kuma bayyana Kodinetoci na Kananan hukumomi kamar haka, Alhaji Abdullahi Lokaja Anka, Alhaji Sagir S/Pawa Dambo ,Bakura, Alhaji Mukhtar Lawal B/Magaji, Malam Shehu Abdullahi Bukuyyum, Muhammad Lawal Karekai Bungudo, Alhaji Abubakar kudi kusa Gumi, Hon Yahaya Gusau, Hon Bala Muhammad Magini Kauran Na Moda, Alhaji Lawal Tsara Damaga Maradun, Hon Babangida Bala Mayanci Maru, Babangida Aliyu Waziri Shinkafi, da Abdullahi Musa Mainera Talata Mafara, Alhaji Abdullahi Yusuf ‘Yankuzo Tsafe, da kuma Muhammad Jakada Zurmi.
Anan take dai Kodineta na Jihar,Hon Tanimu Mada ya ba shugabann Kananan hukumomi takarar aka aiki da kuma basu umarnin samar da Shugabanni Na gunduma a fadin Kananan hukumomin.
Amadadin Shugabannin Kananan hukumomin,Alhaji Abdullahi Lokaja Anka ya bayyana godiyar sa ga Allah ya da ya bamu wannan matsayin da akaga muncancanta kuma insha Allah zamu ba marada kunya wajan samun nasara dan takarar mu na Shugaban Kasa Bola Ahmad Tinubu.inji Alhaji Abdullahi Lokaja Anka.
