Jam’iyyar PRP ta rantsar da Shugabannin ta a jihar Katsina
Daya daga cikin jam’iyyun adawa da suka dade a Najeriya ta PRP ta rantsar da sabbin Shugabannin ta na jihar Katsina.
Taron rantsarwar wanda ya gudana a ofishin jam’iyyar dake garin Katsina ya samu halartar dukkan sabbin zababbun jam’iyyar da kuma dumbin magoya baya.
Da yake jawabi jim kadan bayan rantsuwar, sabon Shugaban jam’iyyar, Hassan Hamisu Kankara, ya bayar da tabbacin tafiya da kowa da kowa domin samun nasarar jam’iyyar a zabukan masu zuwa.
Hassan Hamisu ya kuma kara da kira ga matasa su shigo jam’iyyar ta PRP domin bayar da tasu gudummuwar.
Shugaban jam’iyyar ya kuma ayyana cewa burin su a zaben da ke tafe shine na lashe zaben Gwamna da kuma akalla kaso 2 bisa 3 na yan majalisun jihar.
Tun da farko jami’in da jam’iyyar ta turo daga hedikwatar ta ta Abuja Alhaji Musa Muhammad Kankara ya yi kira ga ya’yan jam’iyyar su kasance masu akida irin wadda aka san yan jam’iyyar da su.
