Kungiyar tuntuba da sasanci tsakanin ‘ya’yan jam’iyyar PDP ta yi taro tare da karrama Sanata Tsauri
Wata kungiya dake rajin hada kan ya’yan jam’iyyar PDP ta gudanar da babban taron ta tare kuma da karrama tsohon Sakataren jam’iyyar PDP na kasa, Sanata Umar Tsauri.
Katsina Post ta samu cewa taron wanda ya gudana a hedikwatar jam’iyyar ta jihar Katsina ya samu halartar dukkan mambobin kungiyar da kuma magoya bayan jam’iyyar.
Shugaban kungiyar na jiha, Injiniya Danjuma Alti ya bayyana cewa sun yanke shawarar karrama Sanata Tsauri ne saboda yadda ya fidda ya’yan jam’iyyar na jihar Katsina kunya lokacin da ya rike mukamin nasa.
Danjuma Alti ya kuma bayyana cewa tuni kungiyar su ta dukufa wajen tuntubar al’ummar jihar wajen ganin sun shigo jam’iyyar tare da sasanta ‘yan ta wadanda wani dalili yasa aka batamawa.
Tsohon Sakataren na din din na jam’iyyar ya kuma yi ma mahalarta taron albishir da cewa nan ba da dadewa ba za su jagoranci amsar wasu fitattun mutane daga jam’iyyu da dama a kananan hukumomi 9 zuwa jam’iyyar ta PDP.
