September 16, 2026

Kungiyar Zawiyyah Alheri ta gudanar da taron ta na shekara shekara karo na ukku.

0

Daga Abdulrashid Musa Mobile Media Crew

Kamar yadda ta saba gudanar wa, a duk shekara. kungiyar zawiyyah Alheri, a karkashin jagorancin Shugabanta Alh. Hamisu Hara . Ta gudanar da taron shekara shekara na bana a ranar Lahadi 26/12/2021.

Taron na bana, ya gudana ne a babban dakin taro na sakatariyar Hukumar kula da ma’aikatan kananun hukumomin ta Jihar katsina. An gabatar da kasidu a lokacin da ake gudanar da taron.

Wanda sukai magana, akan yadda za’a tafiyar da siyasa da Ilimi. Da kuma yadda za’a shawo kan matsalar bangar siyasa. Tare da samar ma matasa hanyoyin da zasu ciyar da kansu gaba, da kuma yadda za’a magance matsalar tsaro.

Da yake jawabin maraba, shugaban kungiyar ya nuna godiyar sa ga Allah. Wanda ya sake nuna masu wannan rana. Ya kara da cewa tafiyar Zawiyyah Alheri, ya fara yin ta shi kadai, inda daga baya ta koma mutum talatin. Ya zuwa yanzu kuma sai godiyar Allah.

Malamai masana ne suka tofa albarkacin bakin su a lokacin taron. Daga ciki akwai Dakta Yahuza Ahmed Getso. Wanda ya yi magana akan matsalar da matasa suke a ciki. Da Kuma yadda suka taimaka wajen tabarbarewar tsaro a arewa cin kasar nan.

Shehin malamin addinin nan Sheik Haruna Rasheed Makarfi. Ya yi magana akan yadda ilimi yake da tasiri a cikin harkokin siyasa. Inda ya nuna Addini da Siyasa abu guda ne. Daga karshe ya yi kira tare da sanar da Shuwagabanni  akan mahinmanci Alkawali.

Shima a na shi jawabin shugaban K34 (Dr) Abubakar Tsanni Mabudi Borgu. Ya yaba da kokarin Kungiya ta Zawiyyah Alheri. Tare da kara karfafama masu gwuiwa akan abinda suka dauko.

Da yake jawabin godiya, babban bako sakataran gwamnatin Jihar katsina. Dr. Mustapha Muhammad inuwa. Ya nuna jin dadin sa tare da godema Wannan kungiyar ta Zawiyyah Alheri. Akan yadda suka himmatu wajen wannan hidima, wadda yace bai San yadda suke samo kudin da suke tafiyar da ita ba.

Daga karshe ya yi godiya ga Allah, da ya saka masu da Alheri. Kuma ya yi addu’a ga malaman da suka gabatar da kasidu suma Allah saka masu da Alheri.

Ya kuma roke su da su sake dawo idan dama ta samu domin kara fadakar da Al’umma.

Taron ya samu halartar Dan majalisa mai wakiltar karamar hukumar Dan-MusaHon Aminu Garba Sai baba da takwaransa na karamar hukumar safana Hon Abduljalal Haruna Runka , Karamar hukumar Musawa Hon. Lawal H Yaro Sakataran jam’iyyar Apc na Jihar katsina Malam shitu s shitu. Shugaban bada tallafin karo karatu na jihar katsina Alh. Isah Hame.

Sauran sun hada da shugaban rukunin makera motel Alh. Abba Yusuf. Shugaban sashen kudi da mulki na karamar hukumar Mani. Wasu daga cikin daraktocin daga ofishin na sakataran gwamnatin. Kungiyoyi matasa mambobin kungiyar Zawiyyah Alheri da dai sauransu.

About The Author

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *