Hassan Musa Ya Amsa Kiran Fitowa Takarar Shugaban Karamar Hukumar Funtua A Jam’iyyar APC
Hassan Musa Ya Amsa Kiran Fitowa Takarar Shugaban Karamar Hukuma Funtuwa A Jam’iyyar APC
Daga Hussaini Yero, Funtua
Babban Sakataren mai ritaya na Dumdum-dum A Jihar Katsina, Alhaji Hassan Musa Anda ya amsa kiran Al’umar sa na yin takarar Shugaban Karamar Hukumar Funtuwa da ke Jihar Katsina, karkashin jagorancin Jam’iyyar APC.a Zabe mai zuwa 2025.
Hassan Musa Anda ya bayyana haka ne a ranar Juma’a a Dakin Taro na Marigayi Sarkin Alhazai dake Jabiri cikin Ƙaramar Hukumar Funtuwa .
Ɗan takarar ya bayyana cewa shi mutum ne na Jama’a kuma ba zai watsama duk Mai sanshi da abun alhairi ba Kasa a fuskaba ,dan haka ya ga ya dace ya amsa kiran masoyansa na fitowa takarar Shugaban Karamar Hukumar Funtuwa a Zabe mai zuwa da yardar Allah
Nasan akwai ‘yan takara da yawa amma Jama’a sune alkalai zasu zabi wanda yafi cancanta.kuma wannan takara ban dauke ta ko a mutu ko ayi raiba. inji Hassan Musa Anda”.
Hassan Musa ya yi kira ga magoya bayansa da suyi biyayya da tsarin kundin Jam’iyyar da yada manufofin mu na alhairi ba tare da ɓata wani ɗan takarar ba.
Hassan Musa Anda yayi kira ga al’ummar karamar Hukumar Funtuwa da na Jihar Katsina baki ɗaya da su cigaba da addu’a ga gwamnatin gwamna Dikko Raɗɗa dan ganin kudirinsa ya kai gashi na samun zaman Lafiya da ci gaban Jihar mu da Kasa baki ɗaya.
Ana su Jawaban Shugabanin tafiyar Alhaji Nura Sule ‘Yanɗaki da Muntari Lawal Miloniya Maska sun bayyana Dalilansu na ganin Hassan Musa ya cancanci ya zamo Shugaban Karamar Hukumar Funtuwa da dalilan su kamar haka”.
“A wannan lokaci babu Wandanda yafi Hassan Musa cancanta zamowa dan takarar Shugaban Karamar Funtuwa,Sabo da yadda yasan ta gaba da baya,dan Hassan Musa ya Kwashe tsawon Shekaru 20 ya rike da mukamin Shugaban Ma’aikata na Karamar Hukumar Funtuwa,sannan ya zamo Darakta Mulki sannan kuma ya rike Mukamin na karshe a Matakin Karamar Hukumar Watau (DAF) .
Hassan Musa Anda ya zamo kantoman Kananan Hukumomin Dandume da Safana da Kankara da Karamar Hukumar Sabuwa.dan haka kwararene a sanin Mulki na Karamar Hukumar ta kowane sashe.
Kazalika Hassan Musa ya zamo Babban Sakataren na Dum-dumdum a ma’aikatun Jihar Katsina wanda a nan yayi ritaya.
Dan haka waɗannan dalilai namu sune muka dogara da su na kwarewar sa da jajircewarsa wajan tafiyar da mulki yasa muka huramasa wuta akan ya fito yayi takara a Jam’iyyar mu ta APC dan ya tsamo Karamar Hukumar Funtuwa daga mawuyacin halin da muke ciki”.Inji Kwamandojin yakin Neman Zaɓen
