September 16, 2026

2023: Mutanen Katsina Sun Fi Buƙatar Wanda Zai Kawo Masu Kyakyawan Shugabanci Akan Wanda Zai Ba Su Kuɗi – Joɓe

0

Daga El-Zaharadeen Umar, Katsina

Kwamishinan ma’aikatar kasafin kudi da tsare-tsare na jihar Katsina Hon. Faruk Lawal Jobe ya bayyana cewa yanzu mutanen Katsina sun fi buƙatar mutumin da zai kawo masu shugabanci nagari akan wanda zai ba su kudi.

Hon. Faruk Lawal yana wannan magana ne jim kaɗan bayan da kungiyar matasan Najeriya (Nigeria Youth Congress) suka kawo masa ziyara tare da kiransa da ya fito takarar gwamnan jihar Katsina a zaɓen 2023

Kwamshiinan wanda ya ce ya amsa wannan kira na su, kuma zai cigaba da tuntuɓa domin ganin ya samu nasarar akan abinda jama’a suke ganin zai iya idan aka bashi dama.

“Mutanen jihar Katsina sun san abinda ya kamata saboda duk ɗan siyasar da yake ganin cewa zai sayen su da kuɗi a lokacin yakin neman zaɓe ga fili ga mai doka, a zo a gwada’ inji shi.

Hon. Faruk Lawal Jobe wanda ya ce yana da imanin cewa mutanen Katsina babu abinda suke buƙata a halin yanzu irin wanda zai kawo kyakyawan shugabanci domin magance matsalolin da ake fama da su.

“A matsayina na masanin harkokin kuɗi ban taɓa tsammanin shiga gwamnati ba, balanta riƙe muƙamin siyasa, amma ba yadda Allah bai iya ba, gashi na yi mai bada shawara kuma yanzu ina Kwamishina wannan wani iko ne daga Allah” inji Joɓe.

A cewar sa baya ga tsare-tsaran gwamnatin Masari na Farfaɗo da jihar Katsina da kuma ɗora komi a muhalinsa, da zai cigaba daga inda Masari ya tsaya, ya ce zai yi ƙoƙari so sai wajan ganin ya shawo kan matsalar tsaro da bunƙasa tattalin arziki wanda a wannan fanni ya kware.

Hon. Faruk Lawal Jobe ya ce babu shakka irin rawar da ya taka a wannan gwamnati tasa yasa jama’a ke ganin idan aka bashi dama ya zama gwamna zai ɗora daga inda Masari ya tsaya..

Dangane da batun ajiye aiki ga waɗanda suke riƙe da muƙaman gwamnati kuma suna son yin takara Hon. Jobe ya tabbatar da cewa kwanaki 30 kafin zaɓan fidda gwani zai ajiye mukaminsa na Kwamishina.

Haka kuma ya ƙara da cewa a matsayinsa na masanin harkokin kuɗi yana da dama fiye da saura wajan zamansa gwamnan jihar Katsina wajan zaɓo sabbin hanyoyin samun kuɗin shiga ta yadda zai iya gudanar da gwamnati cikin nasara idan ya samu dama.

About The Author

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *