‘Yan Sanda a Kasar Guinea Bissau Sun Yi Amfani Da Barkono Tsohuwa Wajan tarwatsa Taron ‘yan Adawa
Akalla mutane bakwai ne suka jikkata sakamakon arangamar da ta barke a hedkwatar tsohuwar jam’iyyar da ta mulki kasar Guinea Bissau, mai suna jam’iyyar Afirka don neman ‘yancin kasar Guinea Bissau da Cape Verde a jiya Juma’a.
‘Yan sanda sun yi amfani da hayaki mai sa kwalla da kuma sanduna wajen tarwatsa masu fafutuka daga cikin jam’iyyar mai tarihi da ta jagoranci kasar Guinea-Bissau.
Jam’iyyar ta shirya gudanar da wani taro ne daga yau Asabar zuwa Talata, amma wani bangare da daya daga cikin shugabanninta Bolom Conté ke jagoranta, ba sa jituwa da sauran shugabannin jam’iyyar.
Bolom Conte ya kai kara kotu a watan Fabrairu don kalubalantar hakkin tsohon Firayim Minista, kuma shugaban jam’iyyar tun 2013, Domingos Simoes Pereira, na shirya taron jam’iyyar, yana jayayya da hakan.A cewarsa, wa’adin shugabancinsa jam’iyyar ya riga ya ƙare.
Daga baya kotu ta haramta taron, inda aka umurci ‘yan sandan da su tabbatar ba a gudanar da taron ba, matakin da ‘yan jam’iyyar da masu fafutuka suka nuna adawa da shi.
Jam’iyyar ta (PAIGC), wadda shugabanta Domingos Simoes Pereira ya sha kaye a zaben shugaban kasa na shekarar 2019, na ci gaba da neman sake shiga takara da shugaba Umaro Sissoco Embalo.
An kuma hana Pereira fita daga kasar a karshen watan Fabrairu a wani bangare na binciken da ake yi na yunkurin juyin mulki a shekarar 2021.
Guinea-Bissau, wata karamar kasa ce mai mutane kusan miliyan biyu, tana fama da rashin kwanciyar hankali na siyasa da na soji.
