September 18, 2026

2023: Matawalle Ya Bada Tabbacin Cigaba Da Ayyukan Raya Ƙasa A Zamfara Ta Yamma Idan Aka Sake Zaɓensa

0

Daga Hussaini Ibrahim,Gusau

Gwamnan jihar Zamfara Bello Muhammed Matawalle kuma ɗan takarar gwamna a ƙarƙashin jam’iyyar APC a zaɓe mai zuwa ya tabbatar wa al’ummar mazaɓar Zamfara ta yamma cewa za su gudanar da wasu ayyukan raya ƙasa waɗanda ke da tasiri kai tsaye ga shiyyar.

Matawalle ya bayyana hakan ne a taron yakin neman zaɓen da aka gudanar a garin Bakura shalikwatar ƙaramar hukumar Bakura ta jihar a jiya Laraba.

A cewarsa, kiwon lafiya, ilimi, karfafawa matasa, tsaro da kuma ci gaban al’umma ne gwamnatinsa za ta baiwa fifiko idan aka ba wa wa’adin mulki na biyu.

Matawalle ya buƙaci masu zaɓe da su zaɓe shi domin a ci gaba da gudanar da shugabanci nagari wanda zai iya sa jihar ta yi alfahari da shi wajan samar da cigaban karkara da biranan yankin.

Ya umurci magoya bayan APC da su ci gaba da bin doka da oda domin gudanar da yakin neman zaɓe dan samun nasara.

Ya yabawa ‘ya’yan jam’iyyar APC bisa goyon bayan da suka bai wa majalisar yakin neman zaɓensa a Bakura, inda ya buƙaci su da su ci gaba da tafiya kafaɗa da kafaɗa alokacin yakin nasarar zaɓen.

A nasa jawabin shugaban kamfen na Matawalle kuma ɗan takarar majalisar dattawa mai wakiltar Zamfara ta yamma a zaɓe mai zuwa, a ƙarƙashin jam’iyyar APC tsohon gwamnan jihar Zamfara Alhaji Abdulaziz Yari ya buƙaci ‘yan jam’iyyar APC da su zaɓi Bola Ahmed Tinubu da Matawalle da sauran ‘yan takarar jam’iyyar APC ba tare da angulu da kan zabo ba domin cigaban ƙasa da Zamfara

About The Author

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *