September 17, 2026

2023: An Ƙaddamar Da Rundunar Yakin Neman Zaɓen Hon. Sani Ɗanlami A Katsina

0

A Yanayi na nuna kara da ‘yan uwan taka Hon. Hamisu Gambo ya jagoranci ƙaddamar da kwamitin yakin neman zaɓen ɗan takarar majalisar tarayya mai wakiltar ƙaramar hukumar Katsina ta tsakiya Hon Sani Aliyu Ɗanlami.

Kwamitin wanda ya kunshi mutane goma sha ɗaya (11) kuma aka ƙaddamar da shi a baban ɗakin taro na Paragon Event Centre, da ke Katsina ya samu halartar duk wani mai ruwa da tsaki na ƙaramar hukumar Katsina.

Tunda farko da yake nashi jawabin ɗan takarar majalisar tarayya mai wakiltar ƙaramar hukumar Katsina ta tsakiya Hon Sani Aliyu Ɗanlami ya yi godiya da irin ƙaramcin da aka nuna masa wajan halartar wannan taro.

Ya kuma sha alwashin samar da ayyukan yi ga matasa idan Allah ya bashi nasara lashe wannan zaɓe wanda ya ce tun a farkon zaban sa da aka yi an ga irin abubuwan alherin da ya yi.

Hon. Sani Aliyu Ɗanlami ya yi bitar wasu daga cikin ayyukan alheri da gwamna Aminu Bello Masari ya yi a jihar Katsina musamman ayyukan magudanan ruwa da ya ce ada mutane sun fuskanci matsalar rushewar gidaje da asarar rayuka da ta dukiya.

Ya cigaba da cewa kokarin gwamna Aminu Bello Masari wannan matsala da ake fama da ita ta zama tarihi, yana ba bada tabbacin idan aka zaɓi jam’iyyar APC daga sama har ƙasa za a cigaba da amfana da ribar dimokuraɗiyya a jihar Katsina da ƙasa baki ɗaya.

Daga ƙarshe Hon. Sani Aliyu Ɗanlami ya yi ƙira ga wannan runduna da ta koma gida ta bi lungu da sako domin neman alfarmar al’umma da su zaɓe da kuma duk wanda ya tsaya takara a ƙarƙashin jam’iyar APC.

Da yake jawabi bayan ƙaddamar da wannan kwamiti shugaban ƙaramar hukumar Katsina kuma shugaban kwamitin Hon. Aminu Ashiru Kofar Sauri ya yi matuƙa farin ciki da nuna godiya da aka zaɓe su domin yin wannan gagarumin aiki.

Ya bayyana cewa za su iya ƙoƙarin su domin ganin Hon. Sani Aliyu Ɗanlami da sauran ‘yan takarar jam’iyyar APC sun samu nasarar lashe zaɓe mai zuwa insha’Allahu.

Wannan kwamitin na ɗauke da mutane irinsu Hon Aminu Ashiru shugaban ƙaramar hukumar Katsina a matsayin shugaba wanda zai jagoranci wannan runduna domin samun nasarar zaɓe mai zuwa.

Sauran waɗanda za su rufa masa baya sun haɗa da Hon. Bishir Gambo Saulawa da Babangida Waya da Hon. Babangida Nasamu da Huhu Sulluɓawa da kuma Dikko Bala Kofar Sauri da sauran jama’a.

About The Author

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *