Hukumar NDLEA Ta Kama Wani Mutum Da Kwayar Tramadol 9,140 A Katsina.
Hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa rshen jihar ta samu nasarar kama wani mutum mai shekaru 40 da haihuwa dake sayar da kayan gyara da kwayar tramadol 9140 cikin jihar a ranar 29/12/2022.
Kwamandan hukumar na jihar Katsina Mohammed Bashir lbrahim ya bayyana hakan a lokacin taron manema labarai da ya gudana a shelikwatar hukumar dake cikin birnin Katsina.
Kamar yadda ya ce wanda ake zargin mai suna Ifeanyi Olinya dan asalin jihar Enugu, an kama shi ne a gidansa.
Ya ce biniken hukumar ya taimaka wajen gano karin wasu kwayoyin a cikin motar wanda ake zargin, abinda yasa suka kwace motar da shagonshi.
Kwamandan hukumar ya kuma bukaci al’umma dasu taimaka hukumar da muhimman bayanai domin gudanar da aikin su cikin nasara.
