September 16, 2026

Ƙasar Sin ta hana ƴan ƙwallon ƙafa yin Zane

0

Ƙasar Sin ta hana ƴan ƙwallon ƙafa yin zane a fatar su Ƙasar Sin, wacce a ka fi sani da China ta hana ƴan ƙwallon ƙafa yi zane a jikin su, wanda a ke kira ‘tatoo’ da turanci.Ƙasar ta kuma umarci wadanda su ka yi zaɓen da su yi maza su goge na jikin su domin tarbiyyar masu tasowa a cikin al’umma, in ji Hukumar Ƙwallon Ƙafa ta ƙasar, GAS.

Haka kuma umarnin ya haɗa da hukunci ga masu kunnen ƙashi a kan dokar.”An hana ƴan ƙwallon ƙafar ƙungiyar ƙasar nan manya da ƴan ƙasa da shekara 23 yin zane a jikin su,” in ji sanarwar wacce ta fita a ranar Talata.”Waɗanda su ke da shi a jikin su to su yi maza su cire shi.

Idan akwai wata matsala, to a rufe wajen a lokacin attisaye ko wasa idan kungiyar ta amince da hakan,”Hakazalika hukumar ta hana ƙungiyoyin ƙwallon ƙafa na ƴan ƙasa da shekara 20 ɗaukar sabbin ƴan wasa masu zane a jikin su.Rahotanni sun baiyana cewa ba wannan ne karon farko da ƙasar ke harin hana yin zane a jikin su ba.

About The Author

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *