September 17, 2026

Ƙaddamar da Litattafai: Kungiyar Mun Gani A Ƙasa Ta Sayi Kwafi 9 Akan Dubu Ɗari

0

Daga Maman Faruk

Kungiyar mun gani a kasa karkashin jagorancin shugaba kungiyar Injiniya Suraj Yazid Abukur ta taka rawar ganin wajan ƙaddamar da wannan littatafai guda uku

Litattafan da aka ƙaddamar wanda marubuci Mande Muhammad Kurfi ya rubuta sune Ƙamusun Ingilishi Da Hausa da Magana iyawa ce da kuma In Ɓere da Sata Daddawa da wari wanda kuma taron ya wakana a ɗakin taro na jami’ar Umaru Musa Yar’adua da ke Katsina.

Da ya ke ƙaddamar da sayan litattafai a madadin kungiyar Mun Gani a kasa karkashin jagorancin Injiniya Suraj Yazid Abukur Abdulrahaman Aliyu ya ce sun zo wajan ne domin bada ta su gudunmawa a harkar adabi.

Haka kuma ya kaddamar da litattafan guda tara a kan kudi naira duba dari kuma ya biya nan take tare da fatan alheri ga wannan taron kaddamawa.

About The Author

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *