September 16, 2026

Zirgin cin hancin miliyan 5- Ɗan kasuwa ya kai ƙarar Dambazau kotu

0

Wani ɗan kasuwa a Jihar Kano, Ismail Sani ya kai kai ƙarar Shugaban Hukumar Kare Haƙƙin mai Sayen Kaya ta Kano, CPC, Birgediya-Janar Idris Bello Dambazau (mai ritaya) zuwa Babbar Kotu bisa zargin neman ya bada cin hancin naira miliyan 5.

Jaridar Daily Trust ta rawaito cewa mai ƙarar ya yi zargin cewa CPC ta ƙwace masa man gyaɗar, inda shi kuma shugaban hukumar ya ce masa ya bada naira miliyan 5 sannan a dawo masa da kayan nasa da hukumar ta ƙwace.

Mai ƙarar ya nuna cewa sun yi wannan magana ne ta wayar salula.

Sabo da haka, mai ƙarar ya nemi kotu da ta umarci kamfanin layin sadarwa na MTN da ya fitar da muryar su yayin da shugaban ya ke neman cin hancin miliyan 5 ɗin.

Ya kuma nemi kotu da ta umarci hukumar NAFDAC da ta nuna takardun shaidar tabbatar da ingancin man nasa da CPC ta ƙwace, sannan a kawo duka shidun gaban kotu.

Alƙalin kotun, Nasiru Saminu ya amince da roƙon mai ƙara, inda ya umarci MTN da NAFDAC da su kawo abinda mai ƙarar ya nema a matsayin sheda.

A nashi ɓangaren, wanda a ke ƙara, ta bakin lauyan sa, Barista M. H. Waziri, ya ƙaryata duk ƙorafin da a ka shigar a kan hukumar da shugaban ta, inda ya tabbatar da cewa gaskiya za ta yi halin ta.

Alƙalin ya ɗage sauraron ƙarar zuwa 24 ga watan Janairu, 2022.

About The Author

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *