Zaɓen Fidda Gwani Na APC: Idan Ba A Yi Mani Adalci Ba Zan Iya Ɗaukar Matakin Shari’a – Hon. Jabiru Yau Yau
Ɗan Majalisa mai wakiltar ƙananan hukumar Batsari a majalisar dokokin ta jihar Katsina Hon. Jabiru Yusuf Yau Yau ya yi barazanar ɗaukar matakin shari’a idan har uwar jam’iyya bata yi masa adalci ba.
Hon. Yau Yau ya bayyana haka ga manema labarai a Katsina dangane da abinda ya kira rashin adalci da aka yi a lokacin zaɓen fidda gwani na masu neman takarar kujerar majalisar wakilai ta tarayyar wanda zai wakilci ƙananan hukumomin Batsari da Safana da kuma Ɗan Musa.
” Bayan da aka kammala zaɓen wanda aka ce na samu Kuri’u 49 a yi yin da aka bayyana wand aka ce ya samu nasara da Kuri’u 50 da kuma saura masu takara, sai muka gano akwai matsala a wannan sakamakon” inji shi
Hon. Jabiru Yusuf Yau Yau ya ce sun gano mutane bakwai da ba su samu damar kada Kuri’un su ba, saboda akwai matsala a lissafin masu jefe kuri’a (delegates)
A cewar sa, tuni sun rubuta takardar koke zuwa ga kwamitin da uwar jam’iyya ta kafa kuma ta turo domin sauraren koke-koken jama’a akan zaɓen fidda gwani na majalisar tarayya a jihar Katsina.
“Ina kira ga uwar jam’iyyar mu ta APC da ta yi adalci akan wannan lamari domin a samu adalci, idan kuma ba a yi mani adalci ba, to zan duba matakin da zan ɗauki akan wannan lamari wanda zai iya haɗawa da zuwa kotu” inji Hon Yau Yau
Daga karshe ya yi kira ga magoya bayansa da su kwantar da hankalinsu kadda su tada wata fitina, su cigaba da kasancewa ma su bin doka da oda.
