Zaɓen Fidda Gwani Na APC: An Kashe Biliyan 2 Da Miliyan 750 Wajen Sayen Kuri’a A Katsina – Jam’iyyar NNPP
Daga El-Zaharadeen Umar, Katsina
Babban jam’iyyar adawa ta NNPP a jihar Katsina ta yi zargin cewa an yi amfani da kuɗi na fitar hankali wajan sayen kuri’un Daliget a zaɓen fidda gwani na gwamnan APC da ya gabata.
Shugaban jam’iyyar NNPP a jihar Katsina Hon. Sani Liti ya bayyana haka a lokacin taron manema labarai da aka yi a Katsina.
Hon. Sani Liti ya ƙara da cewa kimanin naira na gogar naira biliyan biyu da miliyan ɗari bakwai da hamsin aka yi amfani da su wajan sayen kuri’un Daliget 1,805 a cikin rana ɗaya kawai.
“Idan har gwamnatin bata ɗauki mataki akan wannan al’amari ba, to ba a san inda wannan ƙasa zata faɗa ba a sakamakon muzanta darajar naira da gwamnati ta taimaka aka yi a Najeriya” in ji shi
Sannan ya ƙara da cewa suna da duk wani bayani na iri kuɗaɗen da aka kashe wajan zaɓen fidda gwani na jam’iyyar APC wanda mutum tara suka tsaya takara. Sai dai ya ce cikekken bayani na nan tafe nan gaba.
Haka kuma jam’iyyar NNPP ta yi koken cewa gwamnan babban bankin Najeriya Mista Godwin Emefele ya faɗa siyasa wanda hakan ya ci karo da dokar ƙasa, ya ce ya kamata ya sauka daga aikin sa tun kafin wuri ya kore masa.
Hon. Sani Liti ya ce ta inda za a tabbatar da wannan ikirari na su shi ne, yadda shugaban baban bankin Najeriya ya yi amfani da kuɗi naira miliyan 100 wajan fom ɗin takarar shugaban ƙasa a kakar zaɓen da ake ciki.
Jam’iyyar NNPP ta ce baya ga sayen fom da shugaban baban bankin Najeriya ya yi, ya kuma sayi motoci 100 da zai yi amfani da su wajan yakin neman zaɓe kafin ya janye takarar sa.
Hon. Sani Liti ya ce kasancewar Godwin Emefele ɗan wata jam’iyyar kawai ya haramta masa cigaba da zama gwamnan baban bankin Najeriya, ya ce idan kuma hakan bata samu ba, shugaban ƙasa da kansa ya kamata ya nuna halin girma da mutunci wajan sauke shi daga kujerarsa.
Kazalika jam’iyyar NNPP ta yi zargin cewa Godwin Emefele yana da hannu dumu-dumu wajan faɗuwar darajar naira a Najeriya wanda ke neman kassara kasar ta fuskar tattalin arziki.
