Zargin Rashawa: Kotu Ta Bada Umarnin Kwace Wata Jami’a A Kaduna.
Wata babbar kotun tarayya da ke zamanta a Abuja, a ranar Larabar nan, ta ba da umarnin kwace kadarorin jami’ar NOK dake jihar Kaduna na wucin gadi.
Jami’ar wadda tsohon Daraktan kudi a ma’aikatar lafiya ta tarayya Anthony Hassan ya gina, ana zargin an gina ta ne daga kudaden haramun da aka samu ga mai ita.
Hassan wanda daraktan kudi ne a ma’aikatar tsakanin 2016 zuwa 2019, ana zargin ya gina Jami’ar ne ta hanyar damfara.
Kadarorin Jami’ar da aka kwace sun hada da ginin hukumar gudanarwa, ginin ICT, tsangayar harhada magunguna, bangaren kimiya, gine-ginen Ilimi guda biyu, dakin karatu da sauran gine-gine.
Sauran kadarorin da aka gano ga Hassan wadanda kuma aka kwace sun hada da kamfanin ruwa mai suna Gwasmyen Water Factory, cibiyar taro ta Gwasmyen Event Center da kuma otel din Gwasmyen International Hotel da ke Kaduna.
Alkalin kotun, Mai shari’a Zainab Abubakar, ta bayar da umarnin kwace kayan na wucin gadi a lokacin da take yanke hukunci kan karar da hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa (EFCC) ta gabatar.
Lauyan EFCC, Ekele Iheanacho, ya shaida wa kotun cewa hukumar ta nemi wannan umarni ne “bisa ga sashe na 44 (2) na kundin tsarin mulkin tarayyar Najeriya na shekarar 1999 (wanda aka gyara) da kuma sashe na 17 na kudin laifukan zambar kudade da sauran laifuffuka mai lamba 14, 2006.
Hukumar ta bakin jami’ar bincikenta, Adaora Asabe Oragudosi, ta binciki wasu bayanan sirri da aka tabbatar da suka hada da hada baki, sata, cin zarafin ofishi da kuma karkatar da kudade ga wasu ma’aikatan ma’aikatar lafiya ta tarayya inda aka gano kadarorin da aka bayar da umarnin a kwace ga wanda ake tuhuma.
A hukuncin da kotun ta yanke, kotun ta bayar da umarnin a buga wannan umarnin a jaridu na kasa masu fita kullun na kwace kadarorin na wucin gadi, tare da sanar da duk mai abun cewa kan kadarorin da ya nuna dalilinsa, a cikin kwanaki 14, dalilin da ya sa ba za a ba wa gwamnatin tarayyar Najeriya ba.
Mai shari’a Abubakar ta dage sauraron karar har zuwa ranar 5 ga watan Oktoba, 2022, domin kara zama.
Jaridar LEADERSHIP ta bada rohotan cewa dai, jami’ar mai zaman kanta watannin baya ne gwamnatin tarayya ta amince da ita.
