Zargin Kungiyar ‘Yan Jarida Reshen Abuja Akan Gwamna Masari Ba Gaskiya Ba ne.
Daga El-Zaharadeen Umar, Katsina
An ja hankali gwamnatin jihar Katsina dangane da wani batun na kungiyar ‘yan Jarida ta kasa reshen Abuja da ta zargin gwamna Aminu Bello Masari da bada umarnin kama wani mai suna Nelson Omonu da ke aikin a jaridar Summit Post
Wannan zargin dai yana kunshe ne acikin wata sanarwa da kunigiyar ta fitar ta hannun Sakatare da kuma Ciyaman Comrade Emmanuel Ogbeche da Ochiaka Ugwu, suka sanyawa hannun bisa yakinin cewa jami’an tsaron sun yi gaba da Dan jaridar bisa umarinin Gwamna Aminu Masari
Sai dai kuma acikin wata takarda da mai taimakawa gwamna Masari akan harkokin yada labarai, Abdu Labaran Malumfashi ya fitar ga manema labaiai a Katsina ya ce wannan zargi shi ne mafi muni da kungiyar ‘yan jarida ta kasa reshen Abuja ta yi wa Masari, haka kuma kungiyar ta yi kokarin rusa nasara da ake samu akan matsalar tsaro da ta addabi jihar Katsina duk da cewa ba katsina ba ce ka dai ke fuskatantar matsalar tsaro ba.
Ya ce domin a cirewa al’umma shakku kuma su rubuta su ajiye, gwamna Aminu Bello Masari akan kowane irin al’amari da ya shafi gwamnati ko na kashin kanshi, bai taba bada umarnin a kama wani Dan jarida a tsare shi ba, A Abuja ko ma a wane wuri cikin fadin Najeriya.
Abdu Labaran ya kara da ce ‘yan jaridar da ke aikin a jihar Katsina tare da wadanda ke aiki a Najeriya kai harma da wadanda suke zaune a Abuja za su iya bada shiadar cewa gwamna Masari yana daga cikin na kusa kuma baban abokin ‘yan jarida
“Mu a namu bangaran, wannan sanarwa da kungiyar ta fitar a karkashin shugaban kungiyar na Abuja ya kara fito da cewa akwai mai daukar nauyinsu wajan aikata wannan rashin arziki, wanda kuma ya kamata kungiyar reshen Abuja sun jagorancin zagaye na musamman a Kasar baki daya.
Haka kuma ya kara da cewa babu mamaki idan har aka ce wani ya koma daga gefe guda yana biyan wasu domin su gudanar da irin wannan kazamin aikin da ake yi domin dora jama’a saman keken bera
Daga karshe ya ce ba su koyawa mambobin kungiyar ‘yan jarida ta kasa reshen Abuja yadda za su gudanar da aikin su ba, amma dai akwai bukatar su rika tabbatar da al’amari kafin bayana shi zuwa ga al’umma ba wai zargi marar toshe balanta na makama ba.
“Ire-iren wannan soki burutsun babu abinda za su haifarwa wadanda suke kirkirashi illar rage masu kima da rushe darajar aikin jarida baki daya.” Inji shi
