Zargin Ɓata Suna: Bala Abu Musawa Zai Sake Shigar Da Ƙara Don Neman Haƙƙinsa
Mataimaki shugaban jam’iyyar APC na jihar Katsina Alhaji Bala Abu Musawa ya sake bada sabon umarni ga lauyoyinsa da su sake shigar da sabuwar ƙara domin neman hakkin ɓata masa suna.
Kamar yadda lauyoyinsa suka shaidawa majiyar Popular News Hausa cewa sun shigar da ƙara ta farko a gaba wata kotun majistire da ke Katsina inda alkalin kotun ya tsame hannunsa daga shari’ar ba tare da bayyana dalili ba.
Lauyoyin sun ce wanda ke da ƙarar, wato Alhaji Bala Abu Musawa ya basu umurnin su sake wata kotun kuma su shigar da sabuwar ƙarar neman hakkin ɓata suna da akayi masa.
Idan za a iya tunawa wannan rigima ta samo asali ne daga wata takarda da Alhaji Mamuda Lawal ya rubuta, yana koke akan zaɓen fidda gwani na ɗan takarar majalisar wakilai a ƙananan hukumomin Matazu da Musawa da jam’iyyar APC ta yi a watan Mayun da ya gabata.
Alhaji Mamuda Lawal ya yi zargin mataimaki shugaban jam’iyyar APC na jihar Katsina Bala Abubakar Musawa da tada hargitsi a wajan zaɓen wanda har aka samu asarar rai da kuma raunata wasu.
Ita dai wannan takardar koke an mikawa gwamnan jihar Katsina, Aminu Bello Masari da jam’iyyar APC da hukumar zaɓe ta ƙasa INEC da sauran jami’an tsaro domin ɗaukar mataki.
A ƙarar da Bala Abu Musawa ya shigar ta hannun lauyoyinsa wanda kuma aka yi zaman kotun a ranar alhamis ɗin da ta gabata, Alkalin kotun majistire ta uku, Alhaji Abubakar Umar ya tsame kanshi daga shari’ar bisa dalilai na ƙashin kanshi.
Amma yace masu kayrar suna iya neman wata kotun, su sake shigar da sabuwar ƙara domin cigaba da neman haƙƙinsu.
Akan haka, Bala Abu Musawa ya umurci lauyoyinsa su nemi wata kotun su shigar da sabuwar ƙarar, kuma tuni lauyoyin sun ce zasu yi haka cikin satin da za a shiga.
Sai dai kuma wata majiya ta tseguntawa Popular News Hausa cewa ana ta ƙoƙarin yadda za a sulhunta maganar ta bayan fage, ba tare da an shiga kotu ba.
Haka kuma majiyar ta ce har shi Bala Abu ya amince da maganar sulhun, amma bisa wani sharaɗi. Inda ya ce sai Alhaji Mamuda Lawal ya rubuta takardar janye wancan zarge-zarge da ya yi da amsar kuskuren shi da kuma bashi hakuri a takardar da zai rubuta .
“Ni Bala Abubakar Musawa idan har Alhaji Mamuda Lawal ya yi haka zan amince a sulhunta, bisa wancan sharaɗi da na ambata a baya,” inji majiyar
Yanzu dai abin jira a gani shi ne, ko za a sulhunta a tsakanin Bala Abubakar Musawa da Alhaji Mamuda Lawal ko kuwa sai an kai ga gurfana a gaban kuliya banta sabo, Allah masani
