September 18, 2026

Zan Yi Aiki Tukuru Domin Fitar Da Gwaman Jihar Katsina Kunya – Hon. Sani JB

FB_IMG_1773752819631

 

Kwamishinan ma’aikatar ilimi mai zurfi da sana’o’i ta jihar Katsina Hon. Sani JB ya tabbatar da kudirin sa na yin aiki tukuru . ya bayyana haka a lokacin da yake jawabi ga manema labarai jim kaɗan bayan ya shiga ofis a ma’aikatar ilimi mai zurfi da sana’o’i da ke Katsina.

 

Hon. Sani JB ya bayyana cewa ya ji dadi so sai saboda yadda gwamna Raɗɗa ya nuna yana son cigaba da aikin da shi bayan ya shafe shekaru huɗu yana shugaban jam’iyyar APC na jihar Katsina.

 

“Sannan ina ƙara bada tabbacin zan yi aiki tare da ma’aikatan wannan ma’aikata domin samun nasarar da ake bukata bisa tsarin da gwamnan jihar Katsina Malam Dikko Umar Raɗɗa ya ɗora jihar akan ta” inji shi

 

A cewar sa, bada dama ga sauran ma’aikata zai taimaka wajen dinke duk wata matsala da ka iya tasowa ta aiki, inda ya ƙara da cewa yin aiki tare shine babbar nasara.

 

Sai dai a jawabin ta, babbar sakatariya a ma’aikatar ilimi mai zurfi da sana’o’i Hajiya Safiya Yamel ta yi na’am da sabon kwamishinan inda ta bada tabbacin za su aiki tare domin cimma nasara.

 

Ta kuma yi fatan cewa za su aiki tare domin ƙara daukaka darajar ma’aikatar ilimi mai zurfi da sana’o’i kasancewar Hon. Sani JB mutum mai hakuri da san cigaba

 

Daga cikin waɗanda suka yi wa sabon kwamishinan ilimi mai zurfi da sana’o’i Hon. Sani JB rakiya sun haɗa da shugaban ƙaramar hukumar Zango Hon. Babangida Yardaje da shugaban jam’iyyar APC na ƙaramar hukumar Daura, da ‘yan uwa da abokan arziki

About The Author