September 17, 2026

Zamu Ɗauki Nauyin Karatun Duk Wanda Ya Haddace Alqur’ani A Katsina – Dikko Raɗɗa  

FB_IMG_1758722892017
Gwamnatin jihar Katsina ta yi alƙawarin ɗaukar nauyin duk wanda ya Haddace Alqur’ani kuma yana da takardun sikandire masu kyau da zai iya karatun Likita ko Unguwar Zoma a Katsina
Gwamna Malam Dikko Raɗɗa ya a bayyana haka a wajen taron sake fasalin tafiyar da makarantun da allon da islamiyya a Katsina.
Taron wanda hukumar kididdiga ta jihar Katsina ta shirya da nufin gayyato masu ruwa da tsaki akan sha’anin makarantun Allo da islamiyya domin samar da sabon tsarin da zai tafiyar da su a hukumance.
Malam Dikko Umar Raɗɗa ya ce gwamnatin sa ta shirya samar da makarantun tsangaya 34 a faɗin jihar Katsina waɗanda suka haɗa da boko da kuma allon tare da sana’o’i.
“Saboda duk Mace ko namijin da ya haddace Alqur’ani mai girma kuma yana da sha’awar ya cigaba da karatun likita ko unguwar zoma, to zamu dauki nauyin karatun sa tun daga farko har ya kammala digiri” inji shi
Tunda farko da yake jawabi babban daraktan Hukumar kididdiga na jihar Katsina Ferfesa Saifullahi Sani Matazu ya nuna buƙatar da ake da ita samar da sahihan bayanai da za su taimakawa wannan shirin sake fasalin almajiranci a jihar Katsina
Ya kuma ƙara da maƙasudin wannan taro ya biyo bayan wata tattaunawa da suka da gwamna Malam Dikko Raɗɗa wanda ya nuna sha’awar da na taimakawa almajirai a jihar Katsina
A cewar sa, yana kyau a tattara mahimman bayanai game da aikin da ake son yin wanda hakan zai taimaka wajen sanin hakiƙƙanin abinda ake bukata a hukumance.
Ferfesa Saifullahi Sani ya ƙara da cewa akwai kungiyoyin da suka nuna sha’awar su taimakawa wannan shirin na samar da kyakkyawar yanayin koyo da koyarwa a fannin almajiranci a jihar Katsina
Haka kuma ya kira ga Malamai da masu ruwa da tsaki da su baiwa wannan shiri haɗin kai domin nasarar da ake bukata musamman yadda Gwamna ya nuna sha’awar ta ta taimakawa wannan tsarin.
Masana da manyan Malamai sun yi jawabai tare da bada shawarwari ta yadda wannan shiri zai kai ga nasara musamman idan waɗanda aka shirya abin domin sun bada hadin kai.
Daga cikin waɗanda suka yi jawabi sun haɗa da Ferfesa Isah Ali Pantami da Ferfesa Umar Alkali da Sheikh Aminu Daurawa Da Dakta Jabir Mai Hula da kuma Sheikh Nazifi Dahiru Bauchi da Dakta Bashir Usman Ruwan Godiya da sauran su

About The Author