Zamu Sa Ƙafar Wando Ɗaya Da Informers A Zamfara – Matawalle
Gwamna Matawalle ya yi gargadi cewa gwamnatin sa ba za ta amince da duk wani aiki na rashin da’a daga wasu marasa kishin kasa ba, da ke son yin amfani da halin da ake ciki a yanzu domin cin ma manufofinsu na siyasa ba.
Mun lura da karuwar ayyukan masu ba da labari ga yan ta’adda (Informers) da ke haifar da hare-haren ‘yan bindiga da yawa a kan wurare masu rauni.
Za mu dauki tsauraran matakai don magance halin da ake ciki, ciki har da yiwuwar rufe hanyoyin sadarwa, inji shi.
