September 18, 2026

Zaben Fidda Gwani: Matasa a Kano Sun Yi Zanga-Zangar Adawa Da Matakin Gwamnonin APC.

0

Wata kungiya mai suna Concerned APC Youths ta gudanar da zanga-zangar lumana a Kano domin nuna adawa da matakin da gwamnonin jam’iyyar APC mai mulki goma sha daya suka dauka na mika mulki ga Kudancin Najeriya.

Da yake jawabi ga manema labarai a wajen zanga-zangar a wannan Lahadin, jami’in kungiyar, Nura Bebeji, ya ce matakin da gwamnonin suka dauka, shiri ne na ware shugabannin matasa a arewa kamar yadda Yahaya Bello, gwamnan jihar Kogi ya nemi takarar shugaban kasa.

Ya yi bayanin cewa duk wani yunkuri da gwamnonin za su yi na hana ‘yan Najeriya abin da suke so, ba shakka ba zai yi wa jam’iyyar dadi ba a zaben 2023 mai zuwa.

“Mu matasan APC mun dam a Arewa. Mun fito ne don nuna rashin jin dadinmu kan abin da muka ji a kafafen yada labarai na rashin jin dadi da gwamnonin goma sha daya suka dauka na mika ragamar mulki ga yankin kuduncin Najeriya.

“Wadannan gwamnoni sune suka kasa gyara kashi 1 bisa 3 na yankunam dake karkashin miyagu, ‘yan ta’adda, ‘yan bindiga da masu garkuwa da mutane dake ayyukansu a jihohin Kano, Zamfara, Sokoto, Katsina, Kaduna da sauransu, inji jaridar VANGUARD.

“Amma yanzu suna da karfin hada kawunansu domin marawa dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC baya saboda son rai.

About The Author

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *