Yunƙurin Ficewar Sanatoci 20 Daga APC: Ku Nemawa Kanku Mafita Tun Kafin Wuri Ya Kure Maku – Hon. Ɗanlami Kurfi
Kamar yadda rahotanni ke cewa akwai kusan Sanatoci 20 na jam’iyyar APC da ke kokarin ficewa daga jam’iyyar saboda wasu dalilai da suka ƙi bayyanawa.
Wannan dai yana zuwa ne jim kaɗan bayan kammala zaɓen fidda gwani da dukkanin jam’iyyun siyasa suka yi a tarayyar Najeriya.
Sai dai kuma tsohon ɗan majalisar tarayya wanda ya wakilci ƙananan hukumomi Kurfi da Dutsima a 2015 zuwa 2019 Hon. Ɗanlami Muhammad Kurfi na ganin wannan ba ƙaramar dibara ba ce Sanatocin za su yi wa kan su, domin haka shi zai zame masu mafita.
Ya ce ita jamiyyar APC akwai ta da daɗin baki, na cewa duk wanda aka ɓatawa ya yi hakuri, ya zo a kafa gwamnati idan an samu nasara za a saka mashi, ya ce duk karya ce kawai za a shirya ma su.
“Naga shugaban jam’iyyar APC na ƙasa ya je majalisar kila ya je ne, domin ya ba su hakuri ko wani abu makamancin haka, amma dai gaskiyar magana shine kadda waɗannan sanatoci su yi wasa da damar su, idan ba su nutsu da APC ba, su nemawa kansu mafita kawai” inji Hon.
A cewar Hon. Ɗanlami Kurfi ba wata jam’iyya da zata ɗauki irin wannan alƙawari kuma ta cika sai jam’iyyar PDP saboda haka yana ba waɗancan Sanatoci na jam’iyyar APC shawara da su yi wa kansu kiyamul laili tunda wuri su nemawa kan su mafita a siyasa
” Ni ɗin nan, lokacin da ina jam’iyyar APC an yi mani haka, kuma an yi wa wasu, shi yasa nake baiwa sanatocin nan shawara tun da wuri su yi abinda ya kamata idan kuma ba haka ba, za su tuna da wannan maganar da na yi masu.” Inji shi
Hon. Ɗanlami Muhammad Kurfi ya ce idan aka dubi mutane irinsu da suka faɗi zaɓe a shekarar 2019 kuma suka taimaka wajan samun nasarar jam’iyyar APC babu wanda aka tuntuɓa ko daga gwamnatin tarayya ko ta jiha, ya ce in kuma akwai a fito fili a faɗa.
Kazalika ya ƙara da cewa shuwagabannin suna baiwa shafafo da mai da kuma yaron su da ke so muƙami koda ba su taka wata mahimmiyar rawa ba, amma su kan an sha su, sun warke, saboda haka su ma saura su kiyaye domin gudun fadawa tarkon mazanbata.
Ganin cewa shi yanzu ba ɗan jami’yyar APC ba ne, to me ya kai shi tsoma baki cikin al’amarin da ya shafi jami’yyar APC, sai ya kada baki ya ce, ya zama dole ya bada shawara saboda akwai abokan sa a cikin masu neman hawa keken ɓera a jam’iyyar APC
Hon. Ɗanlami Muhammad Kurfi ya ce lokacin da ya yi da za a cigaba da gayawa jama’a gaskiya akan wannan gwamnati saboda kowa ya ji a jikinsa, ba wanda zai sake zaɓen wadancan mutane da ba su da amana.
