‘Yan Bindiga Sun Kona Ofishin Yan Sanda Da Gidaje A Zamfara.
A wannan Alhamis ɗin ne wasu ‘yan bindiga suka kona ofishin ‘yan sanda, shaguna da kuma gidaje uku a kauyen Zugu dake cikin karamar hukumar Bukkuyum a jihar Zamfara.
Sai dai wani shugaban matasa a Bukkuyum, Abubakar Garba, ya ce babu wanda aka kashe yayin harin.
Ya ce bayan harin, mazauna garin da dama sun bar garin zuwa Bukkuyum da wasu kauyukan dake makwabtaka da karamar hukumar Gummi domin neman mafaka.
Zugu itace babbar al’umma ta biyu a karamar hukumar ta Bukkuyum.
“Yan bindigar daga dajin Gando ne suka kai harin. Kuma Abinda wasu daga cikin mazauna garin da suka gudu zuwa garin Bukkuyum suka sanar shi ne: gidajen uku na kusa da ofishin ‘yan sanda ne aka toye.
Mazauna yankin sun ce ‘yan bindigar sun wuce, amma suka dawo suka kai musu hari.
“Abinda suke zato shi ne, ‘yan bindigar sun dawo cikin Zugu ne domin su kashe ‘yan sandan dake kauyen, Saboda sun san cewa ‘yan sandan za su iya amsa kiran gaggawa don haka sai suka yanke shawarar fara kai wa sansanin hari,” inji shi.
Malam Garba ya kuma ce an wawashe shaguna kafin daga bisa a kona su.
Ya ce da yawa daga cikin wadanda suka jikkata sun samu raunukan harbin bindiga ne, yayin da wasu kuma suka samu raunuka sakamakon turmutsitsin da ya barke yayin da mutane ke kokarin tsere ma ‘yan bindigar.
Saidai Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar ta Zamfara Mohammed Shehu bai amsa kira da kuma sakon-kattakwana da aka aike mashi akan batun harin ba, inji Majiyar Popular News Hausa ta PremiumTimes.
‘Yan bindiga dai na ta addabar yankin Arewa maso Yamma da wasu sassan Arewa ta Tsakiyar Najeriya, inda suke ta kashe-kashe, tare da raba daruruwan mutane da gidajensu hadi da satar dabbobi.
Haka kuma, suna korar manoma daga gonakinsu, ga kuma satar dalibai.
