September 18, 2026

‘Yan Takarar Gwamnonin PDP 17 Sun Gana Da Wike.

0

‘Yan takarar gwamna 17 sun gana da Wike don rokon shi ya yafe tare da Goyon Bayan Atiku Ayu.

A wani mataki na sasanta rikicin jam’iyyar PDP, a ranar Talata wasu ‘yan takarar gwamna a jam’iyyar sun gana da gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike.

Wata majiya daga fadar gwamnatin kasar ta bayyana cewa, masu neman kujerar gwamnan daga jihohin Katsina, Sokoto, Jigawa, Kaduna, da kuma wasu jihohi 13 sun gana da Wike a gidansa na kashin kansa dake Rumueprikon a karamar hukumar Obio-Akpor ta jihar, inda suka roke shi da ya marawa dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP Atiku Abubakar da abokin takararsa, Dr. Ifeanyi Okowa, da kuma shugaban jam’iyyar na kasa, Sanata Iyorchia Ayu baya.

Taron wanda ya dauki kimanin awanni biyu ana yi, an ce Wike ya yafe wa Atiku da Ayu.

Wasu daga cikin ‘yan takarar da ke tare da ‘yan takarar gwamnan Katsina, Sokoto, sun hada da: dan takarar gwamnan jihar Lagos a karkashin jam’iyyar PDP, Dr. Olajide Adediran, da takwaransa na jihar Ogun, Mr. Ladi Adebutu.

Majiyar Popular News Hausa ta jaridar Vanguard ta ruwaito cewa, an cimma matsayar ganawa da Wike ne bayan wata ganawa da Atiku a ranar Asabar din da ta gabata. An bada rohoton cewa ‘yan takarar sun yi ganawar sirri da Atiku, sun nuna damuwarsu kan takaddamar.

Majiyar ta ce: “Baya ga kalubalen da ake fuskanta a sassan Jihohi daban-daban, ’yan takarar sun nuna damuwarsu kan rikicin da ke kunno kai a cikin jam’iyyar a matakin kasa baki daya, tare da yin tayin sulhu a kungiyance.

“Sun amince da ganawa da Gwamna Nyesom Wike da masu goyon bayan sa domin ganin an shawo kan rikicin.”

An kuma shirya gudanar da jerin tarurrukan daga ranar Laraba da burin ganin kowane dan jam’iyya ya hau kujerar.

About The Author

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *