November 18, 2026

Yan Sanda Sun Tsafke ‘yan Fashi Mutum 6 Tare Da kwato Naira Miliyan 1.8 a Katsina

0

‘Yan Sanda Sun Tsafke ‘yan Fashi Mutum 6 Tare Da kwato Naira Miliyan 1.8 a Katsina

Rundunar ‘yan sandan jihar Katsina ta ce ta yi nasarar damke gungun wasu ‘yan fashi da makami da suke addabi jama’a da sace-sace a cikin birnin Katsina.

Kakakin rundunar ASP Abubakar Sadiq Aliyu ne ya bayyana haka a lokacin da yake Holan nasarorin da rundunar ta samu a cikin mako guda a shalkwatar ‘yan sanda da ke Katsina

ASP Abubakar Sadiq ya ce rundunar su ta samu lamarin yadda wasu matasa suka addabi unguwar filin Polo da ke cikin birnin Katsina saboda haka ba su tsaya wata-wata ba suka ba za jami’an su inda suka yi nasarar tsafke mutane 6

Ya ƙara da cewa ‘yan fashin da suka kama sun haɗa da Isma’il Hamza ɗan shekara 23 wanda aka fi sani da Dawale da Umar Faruƙ Aliyu da aka sani da da lauya ɗan shekara 20 sai Yasir Jamilu mai shekaru 19 da ake yi wa laƙabi da Game

Sauran sun haɗa da Abu Sufyanu ɗan shekara 20 da aka yi wa laƙabi da Gine da Murtala Abubakar mai shekaru 20 ana kiran sa da Mutu tare da Bello Yusuf da aka fi sani da Yellow mai shekaru 25 dukkan su suna zaune a unguwar filin Polo cikin birnin Katsina

ASP Abubakar ya ce a ranar 30/07/2024 da misalin karfe 10 na dare waɗannan matasan ɗauke da muggan makamai da suka haɗa da wukake da adduna da Gorori sun haura gidan wani mutum mai suna Muntari Abba dan shekaru 45 inda suka yi masa fashin naira miliyan 1.850

“Haka kuma waɗanda matasa da ake zargi a ranar 11/08/2024 sun sake haurawa gidan gidan wata mata mai suna Badiya Mansur yar shekara 20 da wata Fatima Mohammed yar shekara 40suka sace masu tunkiya da Rago da kuma wayar hannu.” Inji shi

Ya ƙara da cewa waɗanda ake zargin suna amfani da abin rufe fuska domin kadda a gane su (Marks) kuma jami’an tsaro sun yi nasarar dawowa da kuɗin Muntari Abba naira miliyan 1.850 sannan waɗanda ake zargi sun amsa yi wannan aika-aika.

A cewar sa, waɗanda ake zargi sun bayyana Bello Yusuf da ake yi wa laƙabi da Yellow a matsayin ma’ajin su, wanda kuma a wajan sa ne aka samu wadancan kuɗaɗai.

ASP Abubakar Sadiq ya yi kira ga al’umma da su rika taimakawa jami’an tsaro da bayanan sirri wanda zai taimaka wajen inganta harkar tsaro a jihar Katsina baƙi ɗaya

About The Author

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *