September 18, 2026

Yadda Jam’iyyar Adawa Ta PDP Ta Gudanar Da Zaɓen Shugabannin ta na Jihar Katsina

0

Yadda Jam’iyyar Adawa Ta PDP Ta Gudanar Da Zaɓen Shugabannin ta na Jihar Katsina

Jam’iyyar adawa ta PDP ta gudanar da zaɓen shugabannin ta a matakin jiha bisa kulawar jami’an tsaro da wakilan hukumar zaɓe ta INEC a shalkwatar jam’iyyar da ke Katsina.

Zaɓen dai yana cikin tsare-tsaren jam’iyyar na tunkarar baban zaɓe da ke take na shugabancin jam’iyyar a matakin ƙasa wanda zai gudana a nan gaba kaɗan.

Kafin wannan rana, jam’iyyar ta gudanar da zaɓen shugabannin a matakin mazaɓo da kuma ƙananan hukumomi yanzu kuma an zabi shugabannin jahohi saura kuma na ƙasa baki ɗaya.

A jawabin sa, shugaban rikon kwarya na jam’iyyar PDP a jihar Katsina Alhaji Musa Abdulkarim Makarfi ya bayyana irin nasarorin da suka samu a lokacin riƙon jam’iyyar tare da nuna gamsuwa da yadda tsarin zaɓen ya gudana.

Alhaji Musa Abdulkarim Makarfi ya ƙara da cewa daga cikin irin nasarorin da suka samu sun haɗa da daidaita tsakanin ‘ya ‘yan jam’iyyar PDP a jihar Katsina.

“Haka kuma mun gudanar da tarurruka tare da naɗa shugabannin mazaɓo da ƙananan hukumomi na riko domin tabbatar da haɗin kan ‘ya ‘yan jam’iyyar PDP a jihar Katsina baƙi ɗaya” inji shi

A cewar sa, an buɗe yi wa sabbin mambobi rijista tare da bada katin shaidar zama ɗan jam’iyyar PDP da kuma tsare-tsaren yadda zaɓoɓokan shugabannin za su gudana tun daga matakin mazaɓa har zuwa jiha wanda aka gudanar lami lafiya..

Shima a nashi jawabin, Sanata Yakubu Lado ƊanMarke wanda shine jigon wannan ɓanagare da suka gudanar da zaɓe, ya bayyana jin dadin sa akan yadda aka gudanar da zaɓen wanda ya kira da matakin samun nasara a zaɓen 2027.

Sanata Yakubu Lado ya yi fatan cewa waɗannan shugabannin da aka zaɓa za su zama sillar samun nasarar jam’iyyar PDP a dukkanin zaɓoɓokan da za a gudanar nan gaba.

“Ita siyasa daman sai an yi nisa irin haka ake gane mai amana, saboda haka ina kira gare ku, da ku kasance masu amana a duk inda kuka samu kanku, ta haka ne kawai za a dade ana damawa da ku a wannan harka ta siyasa” inji

Haka kuma Sanata Yakubu Lado ƊanMarke ya yi martanin a karon farko da kansa akan sa tuka sa katsin da faruwa a farfajiyar jam’iyyar PDP inda ya ce shi ba zai rama duk zagi ko cin mutuncin da ake yi masa ba, shi siyasa ce gaban sa saboda haka baya da lokacin kula masu yi masa zagi da hassada

Da yake jawabi a madadin waɗanda suka samu nasarar lashe zaɓen da aka gudanar ba hamayya sabon shugaban jam’iyyar PDP a jihar Katsina Hon. Nura Amadi ya nuna jin dadi da godiyar sa ga jam’iyyar PDP da kuma jagoran su Sanata Yakubu Lado.

Haka kuma ya yi alƙawarin yin aiki tare domin samun nasarar jam’iyyar PDP a zaɓoɓokan da ke tafe musamman na ƙananan hukumomi da za gudanar a watan Fabrairu shekara mai zuwa.

Hon. Nura Amadi ya yi kira ga ‘ya ‘yan jam’iyyar PDP a faɗin jihar Katsina da sauran shugabannin da aka zaɓe su tare da su haɗa kai domin ciyar da jam’iyyar PDP gaba ta yadda za a sanu nasara baƙi ɗaya.

About The Author

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *