Yan Sanda Sun Cafke Fitaccen Mai Safarar Miyagun Kwayoyi a Katsina
Rundunar ‘yan sandan jihar Katsina ta sanar da cafke wani da ake zargi da safarar miyagun kwayoyi mai suna Jibrin Salisu, mai shekaru 27, a ƙaramar hukumar Funtua da ke cikin jihar
An kama wanda ake zargin ne ɗauke da wasu haramtattun kwayoyi da ake kyautata zaton ƙwayar Diazepam ce.
A cewar rundunar, lamarin ya faru ne a ranar 15 ga yunin 2026 da misalin karfe 12 na rana, lokacin da jami’an ‘yan sanda da ke sintiri domin yaki da laifuka daga ofishin ‘yan sanda na CPS da ke Funtua suka tare shi yayin da yake tuka babur.
Kamar yadda binciken da aka gudanar a gano buhu biyu ɗauke da kwayoyi 2,000 da ake zargin Diazepam ne.
Yayin gudanar da bincike, wanda ake zargin ya amsa cewa wata mata mai suna Faith Eze, mai shekaru 26, ce ta ba shi kayan domin kai su ga wani abokin hulɗa da aka fi sani da “Gurgu”, wanda har yanzu yake gudun hijira.
Bayan samun wannan bayani, jami’an ‘yan sanda suka gudanar da bincike inda suka samu nasarar cafke Faith Eze.
Rundunar ta ce duka waɗanda ake zargin sun amsa laifin da ake tuhumarsu da shi. Haka kuma ta bayyana cewa ana ci gaba da ƙoƙarin kamo wanda ake kira “Gurgu” domin ya fuskanci hukunci tare da sauran waɗanda ake zargi.
Kwamishinan ‘Yan Sandan Jihar Katsina, CP Ali Umar Fagge, ya sake jaddada aniyar rundunar na yaki da safarar miyagun kwayoyi da kuma amfani da su ba bisa ka’ida ba.
CP Ali Umar Fagge ya gargaɗi masu sana’ar sayarwa da rarraba irin waɗannan kwayoyi da su daina, tare da kira ga jama’a da su ci gaba da bai wa jami’an tsaro sahihan bayanai domin taimakawa wajen kawar da masu aikata laifuka daga jihar.
