September 18, 2026

Gwamna Raɗɗa Ya Tattauna Da Shugabannin IPAC Kan Harkokin Tsaro a Katsina

FB_IMG_1781938659374

Gwamnan jihar har Katsina, Malam Dikko Umar Raɗɗa, ya gudanar da wani taron tuntuɓa kan harkokin tsaro tare da kwamitin bada shawara na jam’iyyun Siyasa (IPAC), wanda ya haɗa shugabannin dukkan jam’iyyun siyasa da aka yi wa rajista a jihar.

 

Taron ya gudana a ofishin gwamnan ranar Juma’a domin duba halin tsaro a wasu sassan jihar da kuma ƙarfafa haɗin gwiwa wajen tabbatar da zaman lafiya.

 

A yayin taron, Gwamna Raɗɗa ya yi bayani kan matakan tsaro da ake ɗauka musamman a yankin Matazu da Musawa, inda ya ce jami’an tsaro na ci gaba da gudanar da ayyuka tare da goyon bayan gwamnatin tarayya.

 

Ya yaba wa gwamnatin tarayya bisa irin tallafin da take bai wa jihar wajen yaƙi da ’yan bindiga da sauran masu aikata laifuka.

 

Gwamnan ya jaddada cewa tsaro alhakin kowa ne, yana mai cewa rashin tsaro ba ya bambance jam’iyya, addini ko ƙabila. Ya kuma buƙaci shugabannin jam’iyyun siyasa su ci gaba da ba gwamnati shawarwari da gudunmawar da za su taimaka wajen ƙarfafa matakan tsaro da ake aiwatarwa a jihar.

 

Da yake jawabi a madadin IPAC, shugaban ƙungiyar a jihar, Alhaji Salimu Lawal Boyi, ya yabawa gwamnatin jihar Katsina bisa ƙoƙarin da take yi wajen magance matsalar rashin tsaro.

 

Ya ce taron ya nuna yadda gwamnati ke tafiyar da mulki cikin haɗin kai, tare da neman ra’ayoyin masu ruwa da tsaki wajen samo mafita ga matsalolin tsaro.

 

Boyi ya ba da shawarar kafa kwamitin tsaro na jam’iyyun siyasa domin ƙarfafa haɗin gwiwa tsakanin gwamnati da jam’iyyu, tare da buƙatar ƙara saka hannun jari a shirye-shiryen ƙarfafa matasa a matakin ƙananan hukumomi.

 

Haka kuma ya yaba wa gwamnatin tarayya ƙarƙashin jagorancin shugaba Bola Ahmad Tinubu bisa goyon bayan da take bai wa jihar Katsina wajen yaƙi da rashin tsaro.

About The Author