November 19, 2026

Yan Bindiga Sun yi Yunkurin Mamaye Garin Safana har Sun Raunata ‘Yan Sanda Biyu Da wani Mutum Daya – Yan Sanda  Rundunar ‘yan

0

Rundunar ‘yansandan jihar Katsina ta tabbatar da wani harin wuce gona da iri da ‘yan bindiga suka kai a garin Safana inda suka raunata mutane uku biyu daga cikin su jami’an tsaro ne.

Kakakin rundunar ‘yan Sanda na jihar Katsina ASP Abubakar Sadiq Aliyu ya tabbatar da haka ga manema labarai a Katsina

Haka kuma ya bayyana cewa ‘yan bindigar sun so mamaye garin na Safana a cikin daren jiiya asabar da misalin karfe 6:00 pm na maraice kuma sun zo ne da muggan makamai inda suka fara harbi kan mai uwa da wabi.

Sai dai a cewar sa, baturen ‘yan sanda na Safana ya shirya wata tawaga ta jami’an tsaro inda suka fatataki ‘yan bindigar daga garin Safana.

“A lokacin wannan ɗauki ba daɗi da ‘yan bindiga sun raunata jami’an mu guda biyu tare da wani mutum ɗaya wanda yanzu haka suna asibiti ana basu kulawa ta musamman ‘ inji shi

Ya kuma ƙara da cewa tuni jami’an su, sun bazama domin kamo waɗanda suka kai wannan hari na wuce gona da iri. Kuma tuni an fara bincike akan lamarin.

Shima a nashi ɓangaren ɗan majalisar dokokin jihar Katsina mai wakiltar ƙaramar hukumar Safana wanda shi ne mataimakin kakakin majalisar Hon. Abduljalal Haruna Runka ya tabbatar da faruwar lamarin.

Honarabul Abduljalal Runka wanda ya ce ya zuwa yanzu komi ya lafa, sai dai ya tabbatar da cewa jami’an tsaro sun halaka ‘ yan bindiga da dama wanda sai nan gaba za a ji yawan su.

” Yanzu nan maganar da nake da kai, mun samu labarin cewa an yi wa ɓarayin daji ɓarna so sai, kuma hakan ya faru ne saboda jajircewar jami’an tsaro da kuma dakarun tsaro na ‘Community Watch Corps’

A cewar sa, babu labarin kashe ko mutum ɗaya, sannan ba su yi nasarar sace kowa ba, sai dai sun kutsa kai cikin wani shagon sayar da magunguna sun kwashe masa ciniki.

Kamar yadda Honarabul Abduljalal Runka ya tabbatar ya ce ‘yan bindigar sun zo ne akan mashina kuma mashinan sun fi talatin, amma a cikin ikon Allah jami’an tsaro sun fatatake su.

About The Author

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *