‘Yan Bindiga Sun Sace Basarake A Ondo.
Wasu ‘yan bindiga da ake zargin masu garkuwa da mutane ne, sun yi garkuwa da Oba Clement Jimoh Olukotun, Oloso na Oso, a Ajowa- Akoko, a karamar hukumar Akoko ta Arewa-maso-Yamma a jihar Ondo.
‘Yan bindigar wadanda suka kai samamen da misalin karfe 10:15 na daren ranar Alhamis, sun shiga fadar sarkin da karfin tsiya, tare da suka tafiya da shi wurin da ba wanda ya sani.
Majiyar Popular News Hausa ta jaridar LEADERSHIP ta bada rohoton cewa, ‘yan bindigar sun yi harbe-harbe tare da lalata babbar kofar sarkin domin shiga cikin gidansa kafin su yi awon gaba da shi.
Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar Ondo Funmilayo Odunlami, ta tabbatar da faruwar lamarin, inda ta ce an tura jami’an tsaro domin gudanar da bincike kan harin.
