September 19, 2026

Masu Damfara Akan Yanar Gizo 4 Sun Mutu Sakamakon Yin Mankas Da Kwayoyi A Bayelsa.

0

An tabbatar da mutuwar mutanen hudu da ake zargin masu damfara ne akan yanar gizo wanda aka fi sani da ‘Yahoo Boys’ a ranar Juma’a bayan da suka sha wasu muggan kwayoyi akan hanyar Nasco Egei da ke cikin unguwar Biogbolo a Yenagoa, babban birnin jihar Bayelsa.

A cewar rundunar ‘yan sanda, lamarin wanda ya faru da misalin karfe 12 na safiyar Juma’a, ya zo ne bayan shan kwayoyi wanda ake zargin mutanen sun a lokacin murnar da suke ta samun nasarar ayyukansu.#

Da aka tuntubi kwamishinan ‘yan sandan jihar, Benjamin Okolo, ya tabbatar da mutuwar wadannan matasan guda hudu tare da alakanta mutuwarsu da shan miyagun kwayoyi.

“Sun mutu ne saboda shan kwayoyi. Su biyar ne kuma wanda ya tsira daga cikinsu ya shaida mana cewa sun sha kwayoyi biyu-biyu da kansu, shi kuma ya sha guda ɗaya, hakan ke zama dalilin mutuwarsu, ”in ji CP.

Kwamishinan ‘yan sandan, ya tabbatar wa manema labarai cewa, idan ‘yan uwa da iyalan mamatan suka dage cewa an sanya ma mutanen huɗu guba, to ‘yan sandan za su gudanar da bincike don gano musabbabin mutuwarsu, inji majiyar jaridar Popular News Hausa ta Leadership.

About The Author

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *