‘Yan bindiga Sun Kai Wa Tawagar Shugaba Buhari Hari A Katsina.
Fadar shugaban kasa ta bayyana harin da aka kai ma tawagar motocin shugaban kasa dake kan hanyar zuwa Daura gabanin bikin babbar Sallah da ta hada jami’an tsaro, hadiman shi da kuma yan jarida a matsayin abun bakin ciki
A cewar wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban kasa, Garba Shehu ya fitar, maharan sun bude wa ayarin motocin wuta ne daga inda suka yi musu kwanton bauna amma sojoji da ‘yan sanda da kuma jami’an DSS da ke raka ayarin sun fatattake su.
Ya ce mutane biyu da ke cikin ayarin motocin na samun kulawa saboda kananan raunukan da suka samu, inji majiyar Popular News Hausa ta jaridar Leadership.
Sanarwar ta kara da cewa, dukkan ma’aikata da ababen hawan sun isa Daura, mahaifar shugaban kasar lafiya.
