Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Katsina Ta Tabbatar da Kashe Jami’in ta ACP Aminu Umar
Daga El-Zaharadeen Umar, Katsina
Rundunar’yan sandan jihar Katsina ta tabbatar da rasuwar ɗaya daga cikin manyan jami’an ta ACP Aminu Umar Dayi da wani jami’in guda wanda ‘yan bindiga suka kashe a yau talata a Katsina.
Wannan yana kunshe ne acikin wata sanarwa da rundunar ta fitar wanda kakakin ta SP Gambo Isah ya sanyawa hannu aka rabawa manema labarai a Katsina.
Sanarwar ta ce a yau talata da misalin karfe 11:30 nasafe ne rundunar’yan sanda ta samu rahoton gaggawa da ke cewa an hango ɓarayin daji sama da 300 akan mashina suna ta harɓe-harben bindiga kirar AK 47 da GPMG wanda kuma sun farmaki tawagar ACP Aminu Umar a dajin Zakka a lokacin da suke aikin samar da tsaro a wannan daji da ke cikin ƙaramar hukumar Safana.
Sai dai bisa ƙadarrar Allah ACP Aminu Umar tare da wani jami’in ɗan sanda sun rasa rayukansu a lokacin musayar wuta da ‘yan ta’ada.
Bisa haka ne inji sanarwa kwamishinan’yan sanda na jihar Katsina Idrisu Dauda Dabban a madadin rundunar’yan sanda cikin alhini yake isar sakon ta’aziyarsu ga iyalan mamacin da sauran al’umma.
Daga nan ya ƙara bada tabbacin rundunar’yan sanda na cigaba da yakar ‘yan bindiga har sai sun kawo karshen ayyukan ta’addancin su a jihar Katsina baƙi ɗaya.
