September 18, 2026

Yan Bindiga Sun Kai Farmaki Sun Kwashe Mutum 22 A Katsina

0

‘Yan Bindiga Sun Kai Farmaki Runka Sun Kwashe Mutum 22 A Katsina

‘Yan bindiga ɗauke da muggan makamai sun kai farmaki a garin Runka ta ƙaramar hukumar Safana inda suka kashe mutum 1 suka saubata da dama.

Rahotanni daga garin Runka na cewa ‘yan bindigar sun yi wa garin ƙawanta cikin daren jiya asabar kuma suna ɗauke da manyan makamai inda aka yi hasashen cewa sun kai mutum 100

Ɗan majalisa mai wakiltar karamar hukumar Safana a majalisar dokokin jihar Katsina Hon. AbdulJalal Haruna Runka ya tabbatar da haka a hira da wakinmu ta wayar tarho.

Hon. Runka ya ƙara da cewa ‘yan bindigar sun yi zuwan bazata, a cewar sa, sai da suka shirya suka gayyato wasu kungiyoyin ‘yan bindiga sannan suka kawo hari.

Kamar yadda ya bayyana cewa, mutanen sun Runka sun gaya masa cewa ‘yan bindigar suna da yawa kuma ba a samu labarin zuwan su kamar ake samu idan sun shirya irin wannan ta’asa.

Ya ƙara da cewa ‘yan bindigar sun gayyato dabar kasurgumin Ɗan ta’ada nan da ya yi kaurin suna wato Mohoɗinge da kuma Jan Kare da kuma Dabar Mustapha.

Sauran sun hada ‘yan ta’adda daga yankin Kunamawa da ke ƙaramar hukumar Ɗanmusa domin kawo hari a garin Runka ta ƙaramar hukumar Safana.

‘Kamar yadda muka samu labari, sun zo ɗaukar wasu mutane ne da aka ba su bayanan su, sai dai sun yi rashin sa’a ba su tarar da su ba, saboda haka zuwa yanzu sun tafi da mutane 22 amma ba a gana rantancewa ba”inji shi

Kazalika Hon. AbdulJalal Haruna Runka wanda ya yi bayanin cewa suna zargin akwai ma su ba ɓarayin dajin nan bayanan sirri wanda shi yasa mutanen Runka ba su ji labarin zuwan su ba, sai dai kawai suka gan su.

Sai dai a cewar sa, yanzu al’amurra sun fara dawo cikin garin Runka bayan wannan hari, wanda a wannan karon ba su kone motoci ko gidaje ba kamar yadda suka saba

About The Author

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *