‘Yan Bindiga Sun Halaka Baturan ‘Yan Sanda (DPO) Na Jibia A Katsina
Rahotanni da ke shigawa mana suna cewa ‘yan bindiga dauke da muggan makamai sun yi nasara kashe baban jami’in ‘yan Sanda mai kula da karamar hukumar Jibia a jihar Katsina.
Kamar yadda Rahotanni suke cewa DPO A.A Rano Mai mukamin DSP ya rasa ransa ne a lokacin da’yan bindigar suka Kkai farmaki a garin Magama Jibia a jiya talata da daddare.
Sai dai kuma har yanzu rundunar ‘yan sanda ta jihar Katsina bata yi karin bayani ba game da rasa wannan baban jami’in na ta ba.
Karamar hukumar Jibia na daya daga cikin kananan hukumomin da suke fuskantar hare-haren ‘ yan bindiga a ‘ yan kwanakin nan.
Idan za a iya tunawa a farko wannan watan na Fabrairu suka shiga garin Daddara inda suka kashe mai gari tare da tafiya da wasu mutane da dama.
