Yadda Shelkwatar Tsaro Ta Kasa Ta Raba Kayan Abinci Karo na Farko Ga Mutane 200 A Katsina
Yadda Shelkwatar Tsaro Ta Kasa Ta Raba Kayan Abinci Karo na Farko Ga Mutane 200 A Katsina
Babbar Shelkwatar Tsaro Ta Kasa Ta raba shinkafa ga ma buƙata a katsina domin yin azumi cikin sauki tare da rage masu radadin da ake fuskanta na ƙarancin abinci.

Rabon kayan abinci ya kasance ƙarƙashin haziƙin matashi Malam Lawal BK a jiya lahadi kamar yadda rahotanni suka tabbatar.
A Jiya Lahadi Akayi Rabon Shinkafa Ga Mabukata A Jihar Katsina Daga Defence Headquarters Abuja A Karkashin Jagoranci Matashi Mallam Lawal Bk, Inda Mata Da Maza Sama Da Dari Biyu Suka Halarci Wajen Amsar Shinkafa.

Anyi Wannan Rabon Shinkafa Saboda Duba Da Yanayin Na Azumi Da Kuma Hali Da Al-umma Da Suke Domin Rage Radadi Da Kuma Saukin Rayuwa, Wannan Musamman Acikin Watan Ramadan.
Wannan Rabon Kayan Shine Karo Na Farko Wanda Defence Headquarters Ta Shirya A Karkashin Jagoranci Mallam Lawal Kuma Haka Zalika Za’a Cigaba Da Badawa Lokaci Zuwa Lokaci Domin Samun Ingantattar Rayuwa Ga Al-ummar Kasar Nan.

Muna Fatan Mutananen Da Suka Samu Tallafin Na Kayan Abinci Zasuyi Amfani Da Ita Kamar Yadda Yadace.
Allah Ya Karbi Ibada Mu Baki Daya Ameen.

