Rikicin Sojoji Da Jama’ar Unguwar Chake A Katsina Wasu Abubuwan Da Ba a Sani ba
Rahoton Sirri Daga Shehu Na ALLAH
Kamar yadda bincike ya tabbatar a ta bakin wasu da suka ce a sakaya sunansu, inda suka bayyana cewa a wani ɓangare na unguwar chake, wasu matasa suna sana’ar sayar da kwayoyi da kayan maye, to cikin waɗanda ke zuwa saye harda sojoji,
Aka yi rashin sa’a jiya asabar wasu sojoji sun tsaya saye kamar yanda suka saba, sai kawai aka ji rikici ya ɓarke tsakaninsu, su masu sayar da wannan kayan maye suka fiddo makamansu irinsu adda wuka da sauransu.
Kafin ka ce kwabo su kuma sojoji suka fara da harɓi sama, daga bisani ana haka sojojin nan suka harɓi mutum ukku ana tsammanin mutum ɗaya cikin su ɗa ne ga Malam Umaru kucugu, da aka harba an tafi dashi babu rai amma ba a tabbatar da mutuwarsaba.
Ana cikin haka ne shi kuma wani soja ya taka sawun ɓarawo, bayan waɗancan sojojin sun tafiyar su, shi kuma ya taho saman mashin din sa, su kuuma fusatattaun matasan suka bige shi suka kwace mashin ɗin sa suka kunna masa wuta shi kuma ya yi nasarar tserewa.
Bayan faruwar haka, sai wasu sojoji suka dawo aka cigaba da bata kashi tsakaninsu da matasan sai dai jami’an tsaron ‘yan sanda sun tarwatsa matasan ta hanyar amfani da barkonon tsohuwa.
Wani ɗan kasuwa ya shaida cewa misalin karfe 8:00pm ya biyo titin Chake zuwa Kofar Guga ya hango wuta naci ya sha da ƙyar.
Haka kuma misalin karfe 8:40pm wani mazaunin unguwar chake ya bayyana cewa halin da ake ciki sun kasance cikin halin tagayyara ta inda tsoffi da Yara na sahun gaba wajen Fama da matsalar ɗaukewar nunfashin sakamakon, barkonon tsohuwa da aka harba acikin unguwarmu.
A cewar sa, hakan ya tilastawa wasu barin unguwar ‘yan kasuwa da yawa sun rufe shagunasu saboda tsoron abinda ka Iya faruwa na asarori.
