Yadda Salim Ɗan Shekara 13 Ya Fara Sana’ar Wankin Takalma Domin Ya Tallafawa Iyayensa
Daga Umar Faruk
Salim Abdul-salam yaro ne ɗan shekara 13 da ya fara sana’ar wankin takalma kimanin watanni biyar da suka wuce a unguwar kwado
bayan filin wasa na Muhammad Dikko da ke cikin birnin Katsina domin ya tallafawa Iyayensa.
Salim wanda yanzu haka yake aji daya a makarantar sikandire, ya koyi wannan aiki na wankin takalma a wajan wani mutum da ke sana’ar a bakin hanya kusa da gidansu
Ya kuma ƙara da cewa, ya lura da yadda mai wankin takalma yake aikinsa daki-
daki wanda shima ya riƙa koya a haka, ya ce sai kawai shima ya fara jarabawa mataki mataki inda har ya kai ga koyan wannan aiki cikin ƙanƙanin lokaci.
“Na yi tunani wajan samun kuɗin da zan fara wanann sana’ar da su, wanda na kasa tunkaran iyalaina da batun, amma daga karshe na samu damar farawa da naira 600.” Inji Salim
Haka kuma Salim ya bayyana cewa yana samun naira 200 zuwa 350 duk rana, sannan yana amfani da wani abu cikin kuɗin domin biyar kuɗin abin hawa zuwa makaranta.
“Ina matuƙar farin ciki da nake taimakon kaina da iyayena daga ɗan abinda nake samu da wannan sana’a ta wankin takalma” inji shi
Haka kuma ya bayyana cewa baban gurinsa a rayuwa shi ne ya mallaki kamfanin yin talkama amma yanzu ya tsaya akan sana’ar wankin takalma ne a bakin hanya.
Katsina beat ta ruwaito cewa yadda Salim yake da ƙarancin shekaru, kuma yana kokarin samun abinda zai rayu, idan har zai zamu ƙarfafawa tare da samun dama lallai al’umma zata amfana da shi kwarai da gaske.
