September 18, 2026

Yadda Gaddafi Ya Kashe Abiyar Zaman Mamarshi Mai Ciki Da Diyarta A Kano.

0

Jami’an rundunar ‘yan sandan jihar Kano sun kama wani matashi dan shekara 20 mai suna Gaddafi Sagir bisa zargin kisan abiyar zaman mahaifiyarsa mai suna Rabi’atu Sagir dake da juna biyu da ’yar uwarshi, Munawara Sagir a Fadama Rijiyar Zaki dake cikin karamar hukumar Ungogo ta jihar.

An bada rohoton cewa, Gaddafi ya aikata laifin ne bisa hujjar cewa abiyar zaman mahaifiyarsa ce ke da hannu a cikin halin kuncin da mahaifiyarsa ta fuskanta, wanda ya kai ga rabuwa da mahaifinsa tare da kashe diyar matar a harabar inda ta gan shi a lokacin da yake aikata laifin.

Kakakin rundunar ‘yan sandan Kano, SP Abdullahi Haruna wanda ya tabbatar da faruwar lamarin, ya ce an kama wanda ake zargin ne a wani gini da bai kammala ba a lokacin da yake kokarin tserewa daga Kano.

SP Haruna ya ce wanda ake zargin da aka yi masa tambayoyi ya amsa laifin.

A cewar kakakin ‘yan sandan, “A ranar Asabar da ta gabata da misalin karfe 11:30 na dare ne aka samu rahoto daga mahaifin wanda ake zargi da aikata Sagir Yakubu dan unguwar Fadama Rijiyar Zaki dake cikin karamar hukumar Ungogo ta jihar Kano cewa, ya dawo gida ya hadu da matarsa mai juna biyu mai suna Rabi’atu Sagir ‘yar shekara 25 da ‘yarta mai suna Munawwara Sagir ‘yar shekara 8 da haihuwa a cikin tafkin jini mara motsi. Da hakan ne yayi matukar zargin dansa Gaddafi.

“Bayan samun rahoton kwamishinan ‘yan sandan jihar Kano, CP Mamman Dauda, ya umurci tawagar ‘yan sanda karkashin jagorancin CSP Usman Abdullahi, jami’in ‘yan sanda mai kula da reshen Rijiyar Zaki da su je wurin don garzayawa da wadanda abin ya shafa asibitin Murtala Mohammed dake Kano, inda wani Likitan lafiya ya tabbatar da mutuwarsu.

“Wanda ake zargin mai suna Gaddafi Sagir mai shekaru 20 an kama shi ne a wani gini da ba a kammala ba a lokacin da yake kokarin tserewa daga Kano, kamar yadda majiyar Popular News Hausa ta jaridar Vanguard ta ruwaito.

“A binciken farko da ake yi, wanda ake zargin ya amsa laifin yin amfani da sukuddireba ya daba wa abiyar zaman mahaifiyarsa a wuya da goshinta, sannan ya farma yarta har sai da ta daina numfashi. Ana ci gaba da gudanar da bincike,” a cewar SP Haruna Kiyawa.

About The Author

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *