September 18, 2026

An Yi Walimar Yaye Daliban Da Suka Kammala Hardar Alkur’ani A Danmusa.

0

Daga Abbas Nasir

Babban limamin masallacin Juma’a na Danmusa ya ja hankalin iyaye akan mahimmancin sanya ƴaƴa makarantun Islamiyya domin samun ilimin addinin Islama.

Malam Aminu Umar ya bayyana hakan ne a lokacin walimar yaye ɗalibai makarantar Madarasatul Tarteelul Qur’an Wattajaweed sama 20 da suka yi sauka da hardar Alkur’ani mai tsarki a ranar Asabar 07/01/2023.

Ya shawarci ɗaliban da aka yayen cewa su rungumi dabi’ar karatun Alkur’ani mai tsarki haɗi da sauran litattafan Islama domin fadada iliminsu.

Da yake magana a lokacin walimar yaye daliban, headmastern makarantar Malam Shehu Salisu wanda ya samu wakilcin Malam Hamza Sule, ya bayyana cewa makarantar ta yaye dalibai har kashi 3 tun daga lokacin da aka kafa ta a shekarar 2004.

Ya shawarci matasan yankin su tsunduma neman ilimin Islama dana boko domin zama masu amfani a cikin al’umma.

Shima da yake magana a madadin iyayen yara, Alhaji Saminu Ali ya bayyana jin daɗinshi ga malaman makarantar bisa yin amfani da lokacinsu wajen koya ma dalibai.

About The Author

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *