September 17, 2026

YADDA ƳAN RAMUWAR GAYYA ZA SU ILLATA SIYASAR GWAMNA GANDUJE A ZAƁEN 2023

0

DAGA Bashir Abdullahi El-Bash

-Gwamna Ganduje Ya Fusata Manyan Ƴan Siyasa Da Ƙungiyoyin Matasa Da Malamai Da Attajirai Da Ƴan Kasuwa Da Dattawan Jihar Ta Kano Dama Waɗanda Ada Su Na Tare Da Shi, Yanzu Kuma A Shirye Su Ke Da Su Yi Masa Ramuwar Gayya.

-A Yau Gidan Siyasar Gwamna Ganduje Ya Zama Gidan Siyasar Da Ba A Rarrashi Da Lallami Da Ƙaro Mabiya Sai Dai Korar Wasu.

-Jita-Jitar Komawar Gwamna Ganduje PRP Idan Ta Tabbata Gaskiya Ita Ce Za Ta Tashi Alƙiyamar Siyasar Gwamna Ganduje 2023, Mafita Gare Shi Ita Ce Ya Rungumi Kowa Ya Jawo Kowa A Jiki Ya Dama Da Kowa.

Yau Lahadi, 19 Ga Watan Disamba, 2023.
Mai girma gwamnan Jihar Kano Dr. Abdullahi Umar Ganduje ya na cikin tsaka mai wuya matuƙa duba da yadda matsalolin rigingimun siyasa su ka kewaye shi masu hamayya da shi kuma na ɓangarori daban-daban su ke cigaba da samun galaba a kansa cikin shari’o’in da su ke yi da shi a gaban kotuna.

Duk mai nazari da bibiyar al’amuran yau da kullum zai yarda da ni cewa idan har gwamna Ganduje bai tsaya ya fahimci gyara ba, to ba shakka masu shirin ramuwar gayya a kansa za su illata siyasarsa a zaɓen 2023.

Waɗannan mutane ƴan ramuwar gayya asali mutanensa ne, tare da su aka yi komai har ya zama abin da ya zama, amma daga bisani an watsar da su, ana yi babu su.

Daɗi da ƙari akwai kuma gungun rukunoni daban-daban na al’umma kamar ƴan ƙungiyoyin ɗalibai da na wasu daga cikin manyan malaman addini da ƴan kasuwa dana Dattawan jihar Kano dana siyasa waɗanda duk an ɓata musu, kuma lokaci su ke jira su ɗauki fansa.

Yanzu haka jita-jita ta yi ƙarfi cewa akwai iyuwar gwamna Ganduje zai koma PRP ya bar APC, duk da cewar wannan labari ne marar tushe, furofaganda ce kawai ta siyasa daga wasu, amma duk da haka ina tabbatar da cewa wannan shi ne kuskure mafi girma da gwamna Ganduje zai aikata idan har ya yi kuskuren barin APC.

Illa ta farko dole uwar jam’iyyar APC za ta yi wa ƴan majalissun Jiha alƙawura tare da matsa musu lamba su tsige shi, kuma nan take za su tsige shi, daga baya kuma hukumomin bincike irinsu EFCC za su hau nasu aikin a kansa.

Kasancewarsa gwamnan da ke fama da zarge-zarge kala-kala kan harkokin kuɗi, hakan zai sa ya ma rasa lokacin siyasa, ya koma fama da zirga-zirgar kare kai, daga nan ya zama tarihi a siyasar ƙasa da Jiha.

Mafita ga gwamna Ganduje ita ce: ya tsaya ya fuskanci gyara, ya baza hannu ya janyo duk mutanen da aka ɓatawa, ya rungumi kowa da ƴan kowane gida da ƴan kowane tsagin siyasar APC ya dama da su.

Ya yi ƙoƙarin ɗinke kowacce ɓaraka ya zamar da gidan siyasarsa gidan siyasa mai yawan jawo ƙarin mabiya ba faɗa da kora ba. Idan hakan ta faru akwai iyuwar a samun zaman lafiya a siyasar Kano sannan kuma farin jini da kimar mai girma gwamna za ta iya dawowa.

About The Author

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *